An hana sallar Juma'a a masallacin birnin Kudus

'Yan sandan Isra'ila Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu 'yan sandan Israila biyu sun mutu bayan wasu 'yan bindiga Larabawa 'yan kasar Israila sun bude musu wuta a birnin Kudus.

'Yan sanda dai sun bi 'yan bindigan har cikin masallaci mai tsarki inda suka kashe maharan su uku.

An kuma raunata wani dan sanda.

Palasdinawa dai, ko kuma Larabawa mazauna Isra'ila na kara kaimi wajen kai hare-hare da wuka, da harbe-harben bindiga, da kuma na kananan motoci a Isra'ila tun shekarar 2015.

'Yan sandan sun ce mutune ukun da suka kai harin na ranar Juma'a 'yan shekaru 19 zuwa 29, sun kuma ce maharan sun zo ne daga birnin Umm al-Fahm da ke arewacin Isra'ila, kuma jami'an tsaron kasar sun ce ba su da wata masaniya game da maharan a baya.

A wani matakin da ba a saba gani ba, 'yan sanda sun rufe masallacin Baitul Mukaddas inda aka hana yin Sallar Juma'a, matakin da masu wa'azi suka ce babu wani mahaluki a duniya da zai hana su.

A tattaunawarsu ta wayar tarho da Firai Minista Benjamin Netanyahu, Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi Alla-wadai da harin.

A baya dai Mista Netanyahu ya sha zargin shugaban na Palasdinawa da rashin yin tur da irin wadannan hare-hare.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar Palasdinawa ta Hamas, wacce ke kaddamar da hare-hare a yankin Gaza, ta yaba da kai harin da cewa "martani ne ga hare-haren da yahudawa ke kai wa".

Harin dai na zuwa ne makonni bayan an daba wa wata 'yar sandar Isra'ila da wuka, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta, da kuma harin bindiga da wasu Palasdinawa uku suka kai tsohon birnin wanda gabar yamma da Kogin Jordan ya mamaye.

Akalla 'yan Isra'ila 44 da 'yan kasashen waje biyar ne aka kashe a hare-haren da aka dauki kusan shekara biyu ana kaddamarwa.

Isra'ilar dai ta ce Palasdinawa 255 mafiya yawansu maharan aka kashe a tsawon wannan lokacin, yayin da kafafen yada labarai suka ce sauran sun mutu ne a arangama da sojojin Isra'ila.

Labarai masu alaka

Labaran BBC