Kun taba ganin zakanya na shayar da 'yar damusa?

A picture of the lioness Nosikitok nursing a young leopard cub as she lounges in the arid Serengeti Hakkin mallakar hoto Joop Van Der Linde/Ndutu Lodge
Image caption 'Yar damisa na shan nonon zakanya

Abu ne da ba zai yiwu ba a ce 'yar damisa ta goge digo-digon da yake jikinta, amma duk da haka wannan zakanyar ba ta kallonta a matsayin bare.

Wadannan kyawawan hotunan da aka dauka a karon farko suna nuna zakanya tana shayar da 'yar damusa, kuma abu ne mai matukar wahala a samu irin haka.

Hakkin mallakar hoto Joop Van Der Linde/Ndutu Lodge
Image caption Masana sun ce wannan ne karon farko da aka taba ganin haka

Shugaba kungiyar kare dabbobi ta Panthera, Dakta Luke Hunter, ya shaida wa BBC cewa, wannan wani al'amari ne mai matukar mamaki.

Ya ce, "Wani al'amari ne wanda ban taba ganinsa ba, kuma bai taba faruwa ba a tsakanin dabbobi. Mun san cewa ana samun yanayin da zakanya za ta iya daukar 'yar wata zakanyar, amma wannan wani al'amari ne mai rikitarwa".

A cewarsa, "Na san cewa ba wani yanayi da zai sa zakanya ta wani wurin ta dauki 'yar damusa ko ta shayar da ita".

An saba ganin yawancin zakanya suna kashe 'yar damusa idan suka hadu da su, saboda suna kallonsu a matsayin wadanda suke gasar neman abin kalaci.

Hakkin mallakar hoto Joop Van Der Linde/Ndutu Lodge
Image caption Ba a gano 'yar damisar mace ce ko namiji ba, ba ta wuce mako biyu zuwa uku da haihuwa ba.
Hakkin mallakar hoto Joop Van Der Linde/Ndutu Lodge
Image caption Dakta Hunter ya ce, 'yar damisar ta yi sa'a da ba a kashe ta ba.

Dakta Hunter ya ce, zakanyar na da 'ya'ya sa'annin jaririn damisar, wadanda ba su wuce makonni biyu zuwa uku ba.

Zakanyar ta yi nisan kilomita daya daga inda ta boye 'ya'yanta, a lokacin da ta hadu da 'yar damisar.

Kwararru a fanni dabbobi sun yi bayanin cewa ta hadu da jaririyar damisar kuma tana daukarta tamkar 'yarta.

Har yanzu ba a gano inda uwar jaririyar damusar take ba, ko kuma zakanyar na kokarin ci gaba da zama da ita.

Hakkin mallakar hoto Joop Van Der Linde/Ndutu Lodge
Image caption Idan an yi sa'a 'yar damisar za ta koma wurin uwarta ta ainihi

Labarai masu alaka

Karin bayani