Ra'ayi: Menene fa'idar kayyade iyali?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Menene fa'idar kayyade iyali?

Tsarin iyali ko takaita haihuwa batu ne da ake ta cece-kuce a kai a halin yanzu, musamman a kasashe masu tasowa. Gwamnatoci da kungiyoyin agaji sun yi alkawarin ba da sama da dala biliyan biyu, domin samar da magungunan hana daukar ciki ga wadanda ke bukatar tsara iyalin. Tuni da ma wasu suka rungumi wannan tsari, wasu kuma suka ce ba da su ba. To ko me ya sa gwamnatoci da kungiyoyi suke kashe makudan kudade a kan tsarin? Mene ne alfanu ko rashin alfanun tsarin iyalin? Batutuwan da aka tattauna a filin Ra'ayi Riga kenan.