Lazio na zawarcin Lucas Leiva na Liverpool

Lucas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Liverpool Jurgen Klopp yana amfani da Lucas ne a matsayin dan wasan baya, maimakon na tsakiya da tsohon kocin din kulob din Brendan Rodgers yake yawan ba shi

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta bai wa dan wansanta Lucas Leiva damar fara tattaunawa da kulob din Lazio na Italiya kan batun komawarsa can.

Lazio ta yi tayin sayen dan wasan bayan nan ne a kan fam miliyan biyar.

Sai dai dan wasan mai shekara 30 bai buga wasan da Liverpool ta yi da Wigan ba a ranar Juma'a.

Kwantiragin dan wasan wanda dan asalin kasar Brazil ne zai kare a Liverpool ne a kakar badi.

Ya yi wa Liverpool wasa 346 ciki har da wasa 247 na Gasar Firimiya.

Lucas ya koma Liverpool ne a shekarar 2007 daga kulob din Gremio na Brazil a kan fam miliyan biyar, kuma shi ne dan wasan da ya fi dade a Liverpool a halin yanzu.

Labarai masu alaka