Shahararriyar masaniyar lissafi a duniya, Maryam ta rasu

Professor Mirzakhan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Maryam Mirzakhan, Farfesa ce ta lissafi, kuma tayi fice a duniya

A Iran, ana ci gaba da yin Allah wadai da yadda 'yan siyasa da kuma kafafen yada labarai ba su dauki labarin mutuwar shahararriyar masaniyar lissafi a duniya 'yar kasar, Maryam Mirzakhani da muhimmanci ba.

Maryam Mirzakhani ta yi fama ne da cutar sankara, sannan ta rasu a Amurka inda take da zama.

Shekarunta arba'in, kuma ita ce mace ta farko da ta taba samun kyautar Nobel kan ilimin lissafi.

Mutane a Iran sun yi ta nuna rashin jin dadinsu a shafukan sada zumunta, kan yadda kafafen yada labarai na Iran suka ki nuna hotunan matar wadanda ba ta sanye da lullubi, ganin cewa ta zabi yin rayuwa irin ta kasashen Turai ne.

Mutane sun kuma soki irin sakon ta'aziyya da gwamnatin Iran din ta mika, abin da suka ce, irin shi ne ke sa hazikai a kasar, kamar Maryam Mirzakhani yin gudun hijira.