An yi wa Jocob Zuma tayin kudi a kan ya sauka daga mulki

South Afirca Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Afirka ta Kudu ya dade yana fuskantar zargin cin hanci

Rahotanni daga Afirka ta Kudu sun ce an yi wa shugaban kasar Jocob Zuma tayin afuwa da za a bashi dala miliyan dari da hamsin, saboda ya sauka daga kan mulki.

Rahotannin sun ce wani bangare na jam'iyyar ANC mai mulki a kasar wanda ke so mataimakin shugaban kasar ya zama shugaba, ya ce sai samar da kudaden indai shugaban ya amince zai sauka.

Wannan zai iya kasancewa tayin afuwar da kudi mafi girma da aka taba yi wa wani shugaba mai ci a kan ya sauka.

Daya daga cikin sharuddan yarjejeniyar shi ne idan shugaba Jocob Zuma ya amince ya sauka, za a janye tuhume-tuhume fiye da dari bakwai na zargin cin hanci da ake mushi.

Hakan na nufin Mista Zuma din ba zai taba bayyana a gaban kotu ba.

Makudan kudaden da ake so a ba shugaba Zuma, ba daga asusun gwamnatin kasar za su fito ba, wasu 'yan jam'iyyar shi ne suke fatan tara su.

Sai dai babu tabbaci ko shugaba Zuma din zai amince da tayin da aka mushi---wasu rahotanni ma sun ce tuni ya yi watsi da shi.

Babu tantama dai, jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudun ta na fuskantar karin rabuwar kai a tsakanin 'ya'yanta gabanin babban taronta a watan Disamba.