Mutum takwas 'sun mutu' a filin wasan kwallo a Senegal

Filin wasan kwallon kafa a na Demba Diop Senegal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane sun yi ta kokarin bi ta kan katangar don tsere wa daga fili9n wasan, kafin daga bisani ya rufa

Mutum takwas ne aka bada rahoton sun mutu bayan ruftawar wata katanga a babban filin wasan kwallon kafa a kasar Senegal.

Ana kuma fargabar karin wasu 49 sun samu raunuka.

Hadarin ya faru ne a babban filin wasan kwallon kafa na Demba Diop da ke Dakar babban birnin kasar ta Senegal, lokacin da ake buga zagayen karshe na gasar cin kofin kalubale tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta Stade de Mbour and Union Sportive Ouakam.

Kafafen yada labarai da dama sun bada rahoton cewa fada ne ya barke tsakanin magoya bayan kungiyoyin masu fafatawa da juna, inda 'yan sanda suka mayar da martani da harba hayaki mai sa kwalla, da ya haifar da rudani.

Wani likitan gagggawa da ke aikin ceto, da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Senegal ne suka tabbatar wa da BBC adadin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wasu magoya bayan 'yan wasan kwallon sun rika jefa duwatsu da sauran tarkace.

Hotunan da aka rika yada wa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane ke kokowar hawa ta kan katanga a daidai lokacin da hayaki mai sa kwallan ke tashi.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya bayar da rahoton cewa ma'aikatan kashe gobara sun je gudanar da aiki wajen.

Labarai masu alaka