Mun taimaka wajen nasarar zaben Nigeria a 2015 – Sambo Dasuki

Sambo Dasuki
Image caption Ana zargin Sambo Dasuki da hannu a wata badakalar sayo makamai, zargin da ya musanta

Tsohon Mai ba Shugaban Najeriya Shawara kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki ya ce gwamnatin Goodluck Jonathan ta taimaka wajen nasarar zaben kasar a shekarar 2015, musamman a yakin arewa maso gabashin kasar.

Kanar Sambo Dasuki mai ritaya wanda yake ci gaba da kasancewa a tsare, ya bayyana hakan ne a wani sabon littafin da wani tsohon ma'aikacin gwamnatin kasar Yushau A. Shuaib ya rubuta.

Ya ce: "Idan da a ce ba mu yi wani abu kan yaki da Boko Haram, to da jama'a ba su samu damar kada kuri'arsu ba."

"Babu wata tantama, tsaro da kwanciyar hankalin da muka samar su ne suka ba 'yan Najeriya - musamman a yankin arewa-maso gabas, damar zabar gwamnoni da 'yan majalisa da sauransu a babban zaben shekarar 2015," kamar yadda ya bayyana a sabon littafin mai suna: Boko Haram Media War - An Encounter with the Spymaster.

An umarci Nigeria ta biya Dasuki diyyar N15m

Ana zargin Jonathan da karbar 'cin hanci'

Sanatoci ba sa so a yaki cin hanci - Rafsanjani

Littafin mai shafi 308, ya duba rawar da kafafen yada labarai suka taka ne game da yaki da kungiyar Boko Haram.

An kama Sambo Dasuki ne a cikin shekarar 2015 bisa zargin yana da hannu a wata badakalar kudin sayo makamai da suka kai dala biliyan biyu.

Sai dai ya musanta zargin aikata hakan.

Kanar Sambo ya rasa mukaminsa ne bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar da ya gada daga gwamnatin Jonathan a shekarar 2015.

Labarai masu alaka