Tiemoue Bakayoko ya koma Chelsea daga Monaco

Bakayoko Hakkin mallakar hoto Gey
Image caption Bakayoko zai rika sa riga mai lamba 14 ne a Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiyar kulob din Monaco a kan fam miliyan 40.

Ya kulla yarjejeniya shekara biyar ne da zakarun firimiyan.

Dan wansan tawagar Faransar shi ne dan kwallo na biyu da Chelsea ta saya a kakar bana bayan ta sayi Antonio Rudiger daga Roma.

Bakayoko ya koma Monoco daga kulob din Rennes a shekarar 2014 kuma ya fara takawa Faransa leda ne a watan Maris din da ya gabata.

Zai rika sa riga mai lamba 14 ne a Chelsea.

"Ya ni farin ciki sosai da komawa wannan babbar kungiyar. Tun ina yaro nake kallon wasan Chelsea saboda kulob ne da nake kauna sosai tun tasowata," in ji Bakayoko.

Bakayoko mai shekara 22, yana cikin 'yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa yayin da kulob din Monaco ya kai wasan kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai ta bana.

Labarai masu alaka