Isra'ila ta sake bude Haramin Al-Sharif na Masallacin Kudus

jerusalem Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Musulmai kenan lokacin da suke Sallar azahar a wajen HaraminAl-Sharif

Hukumomin Isra'ila sun sake bude bangaren Haramin Al-Sharif na Masallacin Birnin Kudus.

Sai dai Musulmai masu ibada da dama sun ki shiga ciki, saboda sabbin matakan tsaro da hukumomin Isra'ila suka bullo da su.

Shugabannin Musulmai sun ce ba za su shiga cikin Haramin ba saboda na'urorin gane ko mutun na dauke da wani abu mai karfe da hukumomin Isra'ila suka sanya a kofar shiga ciki.

A don haka ne ma musulmai suka yi Sallar azahar a wajen Haramin.

A ranar Juma'a ne hukumomin Isra'ila suka rufe wurin ibadar a karon farko cikin shekaru da dama, bayan an kai hari a wurin.

Wasu larabawan Isra'ila ne suka bindige 'yan sandan kasar biyu--su ma daga baya aka bi su aka kashe su.

Haramin na Al-Sharif, ya na gabashin Jerusalem ne da Isra'ila ta mamaye, wanda ke ci gaba da haifar da takaddama tsakanin Palasdinu da Isra'ila.

Rikicin da ake samu tsakaninsu, yana shafan daukacin yankin a wasu lokuta.