An kama masu sayar da naman doki a zaman na shanu a Turai

horse meat Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A wasu lokuta ana sayar da naman dokin ne a matsayin naman shanu

A kasar Spaniya, an kama mutane fiye da sittin bisa zarginsu da hannu a sayar wa mutane a kasashen Turai da naman doki.

Mutanen suna sayar da naman ne a matsayin naman shanu, sannan a wasu lokutan, naman da suke sayarwar bai dace mutane su ci shi ba.

An kama su ne bayan shekaru hudu ana bincike a kasashe takwas.

Hukumar 'yan sandan Turai ta ce a kasar Ireland ne aka fara tayar da balli, inda gwaje-gwaje suka nuna wasu namomi da ake sayar wa a matsayin na shanu, suna dauke da naman doki.

Jami'ai sun kuma gano cewa dokunan da suka tsufa sosai a Spaniya da Portugal, wadanda bai kamata a ci namansu ba, ana yanka su, sannan a tura namansu Belgium domin sayarwa.

An kama wani dankasuwa dan kasar Holland wanda ake zargi da zama madugun masu sana'ar.