Gobarar tankar mai ta kashe mutane a Cross River

Tankar mai a Najeriya
Image caption Mutum 9 ne suka mutu bayan fashewar bututun iskar gas a Nijeriya

Hukumomi a Najeriya sun fara bincike kan fashewar wata tankar gas a jihar Cross River da ke yankin Niger Delta mai arzikin mai.

'Yan sanda sun ce a kalla mutum goma ne suka mutu, bayan fashewar wata tankar mai a jihar Cross River, lamarin ya janyo gobara.

Yayin da wasu mutane fiye da goma ne kuma aka bayyana cewa sun samu munanan raunuka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da tankar mai ta fashe kuma gobarar da ta janyo ya ke sanadiyyar mutuwar mutane a Najeriya ba.

A wasu lokutan lamarin kan kazanta ne idan mutane sun je domin diban man da ke zuba daga motar, kuma gobara ta tashi da su.

Labarai masu alaka