Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

sojoji na sunturi
Image caption sojojin Najeriya kan aiki

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta gargadi jama'a game da sabon salon da kungiyar Boko Haram ta bullo da shi wajen kai hare-haren kunar bakin wake kan gine-ginen gwamnati.

Mai magana da yawun Rundunar 'yan sandan jihar, Victor Isuku ya shaida wa BBC cewa kananan yaran na kiwo ne a wani daji lokacin da 'yan Boko Haram din suka daura musu damarar bama-baman tare da gargadinsu kada su kwance har sai sun isa gida.

Ya kuma kara da cewa, ''An daura wa Gambo Bukar abin fashewa, kuma suka koma gida da misalin karfe hudu na yamma ba tare da sun bayyana abin da ya wakana tsakaninsu da 'yan ta'addan ba har abin ya fashe kuma ya yi sadanin mutuwar Gambo Bukar din shi kadai.''

Baya ga hakan bam din ya kuma jikkata wasu mutum biyu.

Lamarin ya wakana ne a kauyen Jere da ke jihar Borno.

Harin kunar bakin wake dai ita ce hanyar da har yanzu kungiyar Boko Haram ke amfani da ita sosai wajen kai hare-hare a ciki da wajen kasar.

Lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama tare ci gaba da jefa fargaba a zukatan jama'a.

A watan Afrilun da ya gabata ne wani rahoton da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya fitar ya bayyana samun karuwar amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake a kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Rahoton UNICEF din ya kuma ce an yi amfani da yara 27 akasarinsu mata cikin watanni uku na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da yara 30 da aka yi amfani da su a shekarar da ta gabata.

Labarai masu alaka