Sabuwar rayuwar 'yan gudun hijirar Mali a Niger

Su na koyon ayyukan hannu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yan gudun hijirra kasar Mali a Niger

Daga cikin dimbin 'yan gudun hijirar Mali da ke tsugune a jamhuriyar Nijar, akalla mata 45 ne ke koyon ayyukan hannu daban-daban.

Ayyukan sun hada da koyon dinkin keke, da sake-sake, da yadda ake sarrafa man shafawa, da turare da sauransu abubuwa.

Wata cibiyar ba da agaji ga gajiyayu da ake kira Ibadourahamane, ita ce ta bullo da wannan shirin na bayar da horon ga mata 'yan gudun hijira da ma 'yan mata na sana'oin hannu don nuna musu hanyar dogaro da kansu.

Da dama daga cikin su da ke koyon ayyukan a wannan cibiya tuni suka fara yin amfana, ganin cewa sun fara kwarewa da abun da ake koyar da su.

Nan ba da jimawa ba za su kasance daga cikin masu cin gashin kansu.

Samun wannan horo ya raba su da zaman banza domin sun samu hanyoyin yin sana'o 'i daban-daban da za su basu damar gudanar da rayuwarsu ba tare da sun dogara ga wani ba.

'Yan kasar Mali dai da dama ne daga yankin Menaka maza da mata suka kwarara a birnin Yamai na jumhuriyar Nijar a matsayin 'yan gudun hijira, tun bayan da tashin hankalin da ya barke a arewacin kasar ta Mali sama da shekaru biyar da suka gabata.