Nigeria: Mazauna Abuja sun shiga sabuwar fargaba

jami'an tsaro
Image caption Yan sanda a Abujar Najeriya

Mazauna Abuja babban birnin tarayyar Najeriya sun koka a kan ƙaruwar sace-sace da kwace da cin zarafi da wasu ɓata-gari ke aikata wa ga al'umma a lunguna da tituna musamman da dare.

Rahotanni sun ce ɓata-garin na amfani da rashin wadatattun fitulun da ke haskaka tituna da sauran wurare a birnin domin yi wa jama'a fashi.

A wasu lokuta ma bayan sun kwace wa jama'a kayayyakin da suke dauke da su kamar wayoyin hannu da kudade har su kan raunata jama'a da yi wa mata fyaɗe.

A yawancin lokuta barayin na amfani da wukake ne da kuma sanduna.

Wasu wadanda hare-haren suka rutsa da su a birnin sun shaida wa BBC cewa yanzu mutane ba su da kwanciyar hankali da zarar duhu ya fara.

''Duk yadda gwamnati ta ke zato lamarin ya wuce nan, babu dama duk inda kake yanzu kana sauri-sauri kafin duhu ya yi ka koma gidanka saboda fargaba''

'' Akwai hanyoyi da dama da za ka samu babu wuta, irin wadannan bata-gari sun fi samun mafaka a wurin sai su fito da wukake su ce ka basu waya ko kudi''

Sai dai hukumar 'yan sanda a birnin ta ce tana iya bakin kokarinta domin magance matsalar.

Inda ta kara da cewa ta kama masu aikata irin wadannan na assha da dama, kuma tuni wasu ke gidan yari wasu kuma na kotu inda suke fuskantar shari'a.

Matsalar sace-sacen da kwace-kwace a birnin ta shafi masu motoci har da masu tafiya a kasa ba su tsira ba.

Wasu alkaluma sun nuna cewa bayan birnin Lagos, birnin Abuja ya kasance na biyu wajen fuskantar matsalar kwace a kan tituna.

Amma hukumar da ke kula da birnin ba ta ce komai game da rashin fitulu masu haske a kan tituna a ciki da kewayen birnin ba.

Birnin tarayyar Abuja dai a shekarun baya birni ne wanda a baya mutane kan sakata su wala a ko wane lokaci ba tare da wata fargaba ba.

Labarai masu alaka