Kun san wanda ke zuwa aiki a jirgin sama kullum?
'Yadda nake tafiyar Kilomita 1239 a kullum don isa wurin aiki'
Curt von Badinski injiniya ne kuma shugaban wani kamfanin samar da fasahar rayuwa da ke birnin San Francisco, ya kan yi tafiyar sa'a shida a kullum daga Los Angeles - kuma yawancin tafiyar a jirgin sama ya ke yin ta.
Daga Litinin zuwa Juma'a, ya kan tashi barci tun karfe biyar na asuba, ya nufi filin jirgin saman Bob Hope Burbank inda yake shiga jirgin saman da zai kai shi Oakland, gari mai nisan mil 353 (kilomita 568).
Ya kan ajiye motarsa kusa da dakin Surf Air, wani kamfanin jirgin sama da ke bayar da hayar kananan jiragen sama da a ke biya wata-wata.
Von Badinski na biyan dala 2,300 domin su rika kai shi daga Burbank zuwa Oakland.
Saboda an riga an tantance shi, von Badinski na kauce wa binciken jami'an tsaro, wanda ke ba shi damar shiga jirgin saman cikin mintuna kalilan da isarsa filin jirgin.
Da zaran jirgin ya tashi sama, sai ya fara aiki, ya kan fara da tuntubar abokan harkarsa da suma ke tafiya a jiragen sama, har da wadanda suka bude sabbin kamfanoni da masu zuba jari.
Duk da haka, von Badinski ya san cewa amfani da jirgin saman na da tasiri ga muhalli, shi ya sa ya raba tafiyar gida biyu, yana da mota mai amfani da lantarki domin isa San Francisco daga filin jirgin saman Oakland.
Asalin hoton, Curt von Badinski
Kuma akwai batun bambancin yanayi a wannan yankin, wanda ya kan zama kalubale ga matafiya. A na iya barin Los Angeles cikin ranaku, amma a San Francisco a taras da sanyi da hazo. "A watannin farko lamarin ya shammace ni saboda ban shirya wa sauyin yanayin ba", in ji shi.
Von Badinski na isa ofishinsa da karfe 8:30 kana ya tashi da karfe 5:00, daga nan sai ya nufi filin jirgin sama na Oakland domin ya shiga jirgin saman da zai mayar da shi gida. Zuwa kimanin karfe 9:00 na dare ya isa gidansa a Burbank.
"Yadda nake tabbatar da kashe sa'a shida a kan hanya shi ne na samun damar yin dukkan abubuwan da nake son yi a ko wanne yini.", in ji shi.
"Ina cike da farin ciki a ko wacce safiya."