Malala ta kai ziyara ga mukaddashin shugaban Nigeria

Malala ta yi kira a ceto 'yan matan Chibok Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Malala ta yi kira a ceto 'yan matan Chibok

Fitacciyar yarinyar nan mai fafutikar kare hakkin mata, Malala Yousafzai, ta kai ziyara ga mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.

Malala ta ziyarci Farfesa Osinbajo ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Litinin tare da mahaifinta Ziauddin Yousafzai.

Yarinyar, wacce ta yi suna a duniya bayan harbin da mayakan kungiyar Taliban suka yi mata, ta yi kira ga mahukuntan Najeriya su kara zage damtse wajen bai wa mata kanana ilimi.

Yarinyar 'yar ƙasar Pakistan ta sha yin kira ga shugabannnin Najeriya da kada su gajiye wajen kokarin ganin sun ceto dukkan 'yan matan Chibok.

Kwanannan ne dai Malala ta kammala karatunta na sakandare, sannan ta bude shafinta na Twitter domin ci gaba da fafutikar nemawa mata 'yancin samun ilimi.

A ziyar da ta kai Najeriya, ta jaddada matakin da take dauka na yin amfani da gidauniyarta mai suna Malala Foundation domin tallafawa mata matasa wajen cimma burinsu na neman ilimi.

Labarai masu alaka