Wani 'Ameer din Boko Haram ya mika wuya'

Sojojin Najeriya sun ce wuya ce ta fito da Konto Fanami Hakkin mallakar hoto NIGERIA ARMY
Image caption Sojojin Najeriya sun ce wuya ce ta fito da Konto Fanami

Rundunar sojan Najeriya ta ce wani Ameer (shugaba) na kungiyar Boko Haram ya mika wuya a gare ta inda ya sha alwashin daina ayyukan ta'addanci.

Kakakin rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya fada a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai cewa Konto Fanami, Ameer din Kafa, ya jagoranci reshen kungiyar a yankin Ajigin-Talala-Mungusum.

Ta kara da cewa, "A ranar Litinin ne... hudu daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram sun fito daga maboyarsu inda suka mika wuya ga bataliyar soji ta 120 da ke Goniri.

A cikinsu har da fitaccen dan ta'adda Konto Fanami".

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta kai ga tabbatar da mukamin kwamandan na Boko Haram.

Karanta karin wasu labaran

Janar Kukasheka ya ce binciken da aka yi a kansu ya nuna cewa mayakan na Boko Haram sun fice daga wurin da suke boye ne saboda tsananin wuya da kuma suka gano cewa shugabanninsu ne suka ingiza su.

Sun kara da cewa an ba su gurguwar fassara kan addinin Musulinci da sojojin Najeriya da kuma al'umma, in ji sanarwar.

Ba wannan ne karon farko da sojin ke cewa mayakan Boko Haram sun mika wuya ba.

Sai dai har yanzu mayakan na ci gaba da fafatawa a sassan arewa maso gabashin kasar da dama.

Labarai masu alaka