'Yan Burtaniya sun yi aure na farko a Antarctica

Angon da amaryarsa a kan kankara Hakkin mallakar hoto BAS
Image caption Tom Sylvester ya ce "babu wurin da ya fi wannan dacewa"

A karon farko an daura wa wasu masoya aure, a hukumance, a yankin British Antarctic Territory (BAT), daya daga cikin yankuna mafiya sanyi a duniya.

An daura wa Tom Sylvester da Julie Baum aure a cibiyar bincike ta Rothera Research Station da ke kan tsibirin Adelaide yamma da yankin Antaktika.

Amarya Baum ta sanya kaya masu launin goro wanda ta yanko daga jikin wani tanti, kana an dauki hotunan bikin a yanayi mai matukar sanyin da ya kai -9 Celsius.

Shi kuwa ango Sylvester cewa ya yi, "Yankin Antaktika wuri ne mai matukar kyau kuma mun kulla abokata da mutane a nan."

Ya ce babu wurin da "ya fi wannan dacewa".

"Mun dade muna tunanin yin auren da babu tarin jama'a, amma ba mu taba tsammanin za mu iya yin aurenmu a daya daga cikin wuraren da suka fi kowanne nisa a duniya kamar wannan ba ."

Amarya Baum ta kara da cewa: "Cikin shekara 10 da ta gabata, Tom da ni mun zaga duniya a sanadiyyar aikinmu. Samun damar yin aurenmu a Antaktika kamar wani cikon buri ne."

Hakkin mallakar hoto BAS
Image caption Angon da amaryarsa sun dauki hoto tare da bakin da suka halarci bikin a yanayi ma fi sanyi
Hakkin mallakar hoto BAS
Image caption Masoyan sun fara saduwa da juna shekaru 11 da suka gabata
Hakkin mallakar hoto BAS
Image caption An shirya wannan wurin musamman domin bikin a wannan cibiyar ta bincike

Mista Sylvester ne ya kera zoben tagullar da suka sanya wa juna da kansa a wata makera da ke cibiyar binciken.

Baki kimanin guda 20 ne suka halarci bikin, wanda shugaban tashar, kuma majistiren BAT Paul Samways ya jagoranta.

Shekarun masoyan 11 suna tare, tun bayan wata haduwa da suka yi a wani filin wasa a kasar Wales.

Dukkansu kwararrun mahaya duwatsu ne, kuma su kan koyar da masu sha'awar koyon hawan duwatsu, kana sun yi shekara uku da kulla alkawarin yin aure.

Hakkin mallakar hoto BAS
Image caption Ga amaryar tare da kawayenta suna daukan hotunan bikin auren a kan kankara
Hakkin mallakar hoto BAS
Image caption Wannan shi ne aure na farko tun da a ka yi wa dokar auren yankin gyara
Hakkin mallakar hoto Neil Spencer/BAS
Image caption Mista da Misis Baum sun kafa tarihi a yankin Antaktika

Mista Sylvester dan asalin yankin Sheffield ne, ita kuwa Misis Baum an haife ta ne a Birmingham amma tana zaune ne a Yoxall cikin yankin Staffordshire.

An yi rajistar auren ne a karkashin dokokin yankin BAT, wanda yake karkashin ofishin kasashen Commonwealth, kuma dokar Burtaniya ta amince da auren.

Hakkin mallakar hoto Pete Bucktrout/BAS
Image caption Wannan shi ne hoton cibiyar bincike ta Rotera a kan tsibin Adelaide dake yamma da yankin Antaktika.

Cibiyar Rothera ce ta fi kowace cibiya girma a cikin cibiyoyin da ke gudanar da bincike na kasar Burtaniya.

Angon da amaryarsa sun fara aiki a cibiyar a shekarar 2016 ne.

Cibiyar tana binciken rayuwar halittu ne, kuma ita ce take kula da sauran cibiyoyin da ke yankin Antarktika baki daya.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba