Yadda 'yan sanda suka kashe wata amarya a Amurka

An undated photo of Justine Damond from her personal website.

Asalin hoton, Justine Damond

Bayanan hoto,

Marigayiya Justine ta malamar makaranta ce

'Yan sanda a Amurka sun kashe wata amarya 'yar asalin kasar Australia a birnin Minneapolis na jihar Minnesota.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce "dan sandan da ya yi kisan ya je unguwar ne bayan wani kiran wayar gaggawa da aka yi, inda ya harba harsashin da ya yi ajalin amaryar".

Har ila yau, 'yan sandan sun ce lokacin da al'amarin ya faru ranar Asabar kyamarar da ke gaban rigar dan sandan tana kashe ne.

Kuma sun bayyana sunan amaryar da Justine Damond.

Matar mai shekara 40 tana zaune ne a Minneapolis tare da saurayin da za ta aura.

Justine ta kira lambar gaggawa ta 911 bayan ta ji wata hayaniya a kusa da gidan take, kamar yadda kafar yada labarai ta Australia ta bayyana.

Sai dai wani wanda ya yi ikirarin cewa dan uwan marigayiyar ce ya ce shi ne ya sanar da 'yan sandan abin da ya faru.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Ban san dalilin da ya sa dan sandan ya kashe 'yar uwata ba," in ji mutumin mai suna Zach.

"Ina bukatar amsa. Idan wani zai iya taimakawa, na kira 'yan sanda kuma ina bukatar amsoshi. Na ga ji da irin wadannan tashe-tashen hankula," in ji shi.

Hankali ya tashi

"Wadannan 'yan sandan suna bukatar horon musamman. Akwai bukatar na fice daga nan."

Rundunar 'yan sandan ta ce sun fara gudanar da bincike kuma hukumomi suna so su ga ko akwai hoton bidiyon al'amarin.

Magajin garin Minneapolis Betsy Hodges ya ce "hankalina ya tashi bayan abin da ya faru a daren jiya".

A 'yan shekarun nan, 'yan Amurka na fuskantar kashe-kashe a hannun 'yan sandan wanda hakan yake jawo damuwa a kasar.

Marigayiyar wadda malamar makaranta ce tana daf da daura mata aure.

Ta fara karatun zama likitar dabbobi ne kafin daga bisani ta koma Amurka, inda take zaune tsawon shekara uku.

Alison Monaghan wani wanda ya taba koyar da marigayiyar ya ce "ita ce macen da ta fi kyau" wadda ta taho Amurka don "ta fara sabuwar rayuwa da masoyinta," kamar yadda ya bayyanawa kafar yada labarai ta Australia.

Makwabtanta kimanin 200 da 'yan uwanta duk sun ce abin da ya faru ya tayar musu da hankali kuma sun shirya wani taron alhini don nuna juyayinsu game da rasuwarta.

"Ka tambayi kowa a nan, nuna cikin damuwa ne," in ji wani dalibin marigayiyar.

Ya bayyana marigayiyar da "mutuniyar kirki."

"Ban san wani abu game da yadda dokoki ko 'yan sanda suke aiki ba, amma a ganina, wannan shirme ne. Kana da kyamara a jikinta, me ya hana ka amfani da ita?," in ji shi.

Sai dai 'yan sanda biyun da suke da hannu a kisan sun fara hutun aiki.

Ma'aikatar harkokin wajen Australia ta fitar da sanarwa a madadin iyalan marigayiyar a ranar Litinin.

"Wannan mawuyacin lokaci ne ga iyalinmu. Muna kokarin fahimtar abin da ya faru," in ji sanarwar.