Nigeria: 'Jihohi 30 za su fuskanci ambaliyar ruwa'

Ambaliyar ruwa a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai bukatar hukumomi a Najeriya su kara daukar matakai a kan ambaliyar ruwa in ji masana

Mahukunta a Najeriya sun yi gargadin cewa kusan jihohi 30 ne za su fuskanci bala`in ambaliyar ruwa a bana, sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa.

Masana dai sun bayyana cewa irin wannan ruwan saman alama ce ta tasirin sauyin yanayi ne a kan wasu kasashen Afrika, ciki har da Najeriya.

Wani masani a kan harkokin tsara birane a Nijeriya, Dokta Aliyu Salisu Barau, ya shaida wa BBC cewa janyewar ruwan sama na daga cikin alamun dumamar yanayi.

Ya kuma ce ba al'ummar Nijeriya kadai ba, ita kanta gwamnatin bata shirya wa matsalar yadda ya kamata ba, domin abu ne wanda ya kamata a tsara shi na tsawon lokaci.

'' Mafiya lokuta share magudanar ruwa sai damuna ta kama sannan ake ware kudade a share'', sannan su kuma jama'a suna da mummunar al'adar zuba shara a magudanar ruwa.''

Dokta Aliyu ya kuma kara da cewa yawanci ana yin gine-gine da ba su dace da irin wadannan matsaloli ba, inda a lokuta da dama a kan gina gidaje a hanyoyin ruwa.

Masanin ya kuma ce kamata ya yi a dauki matakan da suka dace a dauka kamar tsara abubuwa ta yadda komai zai tafi yadda ake so, kana akwai bukatar wayar da kan jama'a game da illolin zuba shara a magudanar ruwa.

Inda ya kara da cewa ana yawan samun ambaliyar ruwa da zarar damuna ta kankama a ko wace shekara a Najeriya.

A kan kuma tafka asarar rayuka da dukiyoyi, matsalar kuma kan janyo rashin dubban mastugunai.

Jihohi 16 da ambaliyar ruwa ta yi wa ta'adi sun hada da Ekiti da Osun da Akwa-Ibom da Kebbi,da Naija da kwara da Ebonyi da kuma Enugu.

Sai kuma Abia da Oyo da Legas da Filato da Sakkwato da Edo da kuma Bayelsa.

Labarai masu alaka