Ko yaya farashin kayan masarufi ya ke a Nigeria?

Kasuwar Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kayan abinci har yanzu basu sauko ba acewar wasu 'yan Najeriya

Hukumar ƙidaddiga ta Nigeria ta fitar da sakamakon wani bincike da ya nuna cewa ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyakin abinci idan aka kwatanta da 'yan watannin baya.

To sai dai kuma a bangare guda, ma'aunin farashin kayayyakin abinci da hukumar ta fitar ya nuna cewa babu wata raguwa da aka gani ta fuskar farashin kayan abinci idan aka kwatanta da watannin baya.

Kasuwar Wuse na daya daga cikin kasuwanin babban birnin tarraya na Abuja inda jama'ar birnin da dama kan yi tururuwa a kullum don sayayya.

A lokacin da BBC ta ziyarci kasuwar don duba halin da ake ciki game farashin kayayyakin abinci, bayan hira da masu saye da sayarwa ya kuma gano cewa maganar raguwar farashi tana nan ba ta sauya ba.

Ta bangaren shinkafa dai 'yan kasuwar na ganin rashin shigowa da shinkafar waje a cikin kasar shi ne ya sa har yanzu farashin ta bai koma kasa ba.

A yayin da a bangaren hatsi da wake 'yan kasuwar na cewa rashin shigowa sabon hatsi da wake na bana a kasuwa shi ya kawo rashin saukar farashi kasa -kasa.

Kwano daya na hatsi dai a kasuwar ta Wuse ana sayar da shi ne a kan farashin naira 300, in ji wasu masu sayen kayan abincin.

Wannan abu dai a cewar masu sayar da kayan masarufin ya sa jama'a da dama basu shigowa kasuwar kamar yadda suka saba a baya.

Labarai masu alaka