Nigeria: 'Yadda muka warke daga cutar sikila'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon Samira da Habiba a nan

A baya dai yawancin wadanda suka taba warke wa daga cutar sikila, sun yi hakan ne a Turai, to amma yanzu an fara irin wannan aiki a Najeriya.

Cutar sikila ko amosanin jini na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.

Wata kididdiga da aka fitar a watan Maris din bana ta nuna cewa Najeriya ce ta fi yawan mutanen da ke dauke da wannan cuta a duniya, inda kimanin mutum 91,011 ke fama da ita.

Yankin arewacin kasar ne kuma aka fi samun wadanda ke fama da cutar. Kuma ana alakanta rashin gwaji kafin aure ne babban dalilin da ya sa cutar ke yaduwa a kasar.

Masu fama da cutar kan shafe makwanni a galabaice ba tare da an iya magance musu ita ba, sai dai a ba su magungunan da za su rage radadin kawai.

To ko akwai maganin wannan cuta gaba daya ko kuwa sai dai mutuwa ta raba?

'Na kusa mutuwa'

Habiba Sunusi da Samira Sunusi 'yan uwan juna ne yaya da kanwa uwa daya, uba daya, da aka gano suna dauke da wannan cuta tun suna 'yan wata takwas da haihuwa.

Sai dai sun yi ta fama da cutar inda har akwai lokacin da Samira ta fidda rai da rayuwa, bayan ta shafe shekara bakwai a kwance ba ta ko iya tafiya.

'Yan uwan junan sun shaida min cewa a lokuta da dama tare ake kwantar da su a asibiti daki daya, saboda yadda ciwon yake tasar musu a lokaci guda.

"Wani lokaci fargaba na tayar da ciwon don duk lokacin da na 'yar uwata ya tashi sai tsoro ya kama ni, ai kuwa ni ma a ranar ko washe gari sai nawa ya tashi," in ji Habiba.

Ita kuwa Samira cewa ta yi, "Ni fa duk safiya ta Allah da na farka bacci ba na tashi daga kan gado sai na saurara na ji ko akwai inda zai amsa min da ciwo a jikina.

"Wani lokaci da ciwon ya tasar min ba na ko iya tashi ba na tafiya, sai dai a kwantar a tayar. Na kwanta asibitoci da dama har sai da aka kai ni Saudiyya.

Image caption Samira da Habiba a yayin da Halima ta tarbo su don yin hira

"A can ma na shafe makonni har likitocin suka cewa mahaifana a hakura kawai mu dawo Najeriya don ba wani abu kuma da za su iya. Sai da na yi shekara bakwai a zaune ba na tafiya.

"Mahaifina ya yi ta bincikawa manyan asibitoci na duniya ko za a dace na warke, har daga baya ya samu labarin wani asibiti a kasar Austria da ke aikin dashen bargo ga masu sikila.

Shi ne fa aka kai ni can inda na shafe shekara biyu, ana kokarin magance ciwon kafar da ya jawo min rashin tafiyar."

Samira ta ci gaba da shaida min cewa ita a wancan lokacin gaba daya ta fidda rai da rayuwa, don irin wahalar da ta sha.

Mai rabon ganin badi

To ya ya aka yi saukin ya zo? Ita ce tambayar da na yi wa 'yan uwan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu cutar sikila na fama da shan radadin ciwo

Samira ta ce, "Bayan an yi nasara kafafuna sun mike, sai likitoci suka bukaci a kawo daya daga cikin 'yan uwanmu da muke ciki daya amma wanda ba ya fama da cutar sikila don a debi bargonsa a zuba min.

"Haka kuwa aka yi, kaninmu ya zo aka gwada aka ga ya yi daidai sai aka diba aka sa min. A karon farko abin bai yi ba sai da aka sake sannan aka gwada jinina sai aka ga ya dawo AA a maimakon SS, ma'ana na rabu da cutar sikila.

"Ni da kaina na ji sauyi a jikina don ji na na yi garau kamar ban taba wani ciwo ba. Tafin hannuna da a baya yake fari fat saboda rashin jini sai ga shi ya dawo ja-jawur alamar jini ya wadata.

Ganin haka ne ya sa mahaifinmu ya ce ita ma 'yar uwata Habiba a kawo ta a yi mata, duk da cewa nata ciwon bai kai nawa tsanani ba."

'Ni ma na dace'

To ko ya ya ta kaya ga Habiba da aka yi mata bayan na 'yar uwarta?

"Lokacin da aka yi na Samira duk likitocinmu sun ce ni ba sai lallai an min ba don ciwonta ya fi nawa tsanani. Amma bayan ta samu lafiya da shekara biyu sai ni kuma nawa ciwon ya dinga tashi ganga-ganga, inda dole ta sa ni ma aka kai ni aka yi min.

"A karon farko nawa ya yi ba tare da an sake ba. Kuma yanzu haka dukkanmu rukunin jininmu ya koma AA maimakon SS mai dauke da kwayar cutar sikila.

"Kuma yanzu shekara tara kenan amma ko ciwon kai in dai wanda ya danganci sikila ne to ba mu taba yi ba," a cewar Habiba.

Inda gizo ke sakar

Sai dai fa ba a nan gizo yake sakar ba, don kuwa na tambayi wadannan 'yan uwa ko nawa ake kashewa wajen yin aikin tun da ba ma a Najeriya aka yi shi ba?

Habiba ta ce min ko a wancan lokaci an kashe euro 150,000 ga aikin ko wace daya daga cikinsu, wanda idan aka lissafa a naira ya kai kusan miliyan 25.

A yanzu kuwa kudin yin aikin ya kai euro 250,000 kusan naira miliyan 100 kenan.

"Wannan dalili ne ya sa ba mu faye son gayawa mutane musamman masu ciwon cewa mun warke ba, don sai sun sa rai sun fara jin dadi, sai kuma in suka ji yawan kudin sai su sare."

Sai dai wani abin al'ajabi da suka gaya min shi ne cewa ba a dora su a kan shan wasu magunguna ba kwata-kwata bayan kammala aikin har zuwa yanzu.

'Da sauran rina a kaba'

Sai dai wani hanzari ba gudu ba shi ne cewa duk da Habiba da Samira sun koma AA daga SSa, to ba kuma za su iya auren miji wanda jininsa yake AS ko SS ba.

Ko me ye dalili?

Habiba ta ce, "Likitocin sun ce akwai sauran burbushin cutar kashi biyu cikin 100 a jikinmu wanda hakan ba zai yi wani tasiri wajen saka mana ciwo ba, amma kuma zai iya tasiri ga kwayayen haihuwarmu in har muka auri mai jinsin jini AS ko SS ta yadda hakan zai sa mu haifi yara masu sikila."

Image caption Yanzu haka jinsin jinin Samira da Habiba ya tashi daga SS ya koma AA

Me likitoci ke cewa kan hakan?

Na tuntubi Dakta Najiba Galadanchi wata kwararriyar likitar kan lalurorin da suka shafi jini a asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke Kano, kan ko ya ya take ganin batun wannan dashe duba da labarin Habiba da Samira.

Ta ce min, "Kwarai ana wannan aiki kuma ana dacewa sai dai kawai tsadar sa ke sawa mafi yawan masu fama da cutar ba za su iya zuwa a yi musu ba.

"Sannan kuma ba kowa ake yi wa ba ko a masu cutar sikilar sai wadanda tasu take da tsananin zafi, kamar wadanda ta jawo musu shanyewar wani bari na jiki, ko yawan karin jini."

Dakta Najiba ta kuma ce min ko a Najeriya yanzu haka akwai asibitin da ake wannan aiki a birnin Benin na jihar Edo, kuma likitocin sun yi aikin sau wajen shida, an kuma samu nasara a kan mutum biyu.

Ta kara da cewa idan ana so a kawo irin wannan fasaha ta kafu sosai a Najeriya, to sai gwamnati ta shigo ciki, ta samar da kayan aiki, ta bai wa likitoci horo, sannan ta yi rangwame ga marasa karfi na biyan kudin aikin.

Masana da masu sharhi dai na ganin illar da kuma ukubar da masu fama da cutar sikila ke shiga ta fi ta cututtuka irin su maleriya da HIV/Aids.

Sai dai kuma suna zargin ba a basu kulawa da tallafin da ya kamata.

Labarai masu alaka