Saudi Arabia na binciken macen da ta sanya guntun siket

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon a nan

Hukumomi a kasar Saudiyya na bincike a kan wani bidiyon wata matashiya sanye da guntun siket da guntuwar riga tana yawo a waje.

Matar mai suna "Khulood", mai tallar kayan zayyana ta baza hoton bidiyonta tana yawo a wani gidan tarihi da ke Ushayqir a kasar ta Saudiyya.

Bidiyon dai ya janyo zazzafar muhawara a dandalin sada zumunta, inda wasu suka yi kira da a kama ta saboda keta dokar sanya tufafi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Yayin da wasu kuma suke yaba mata kan abin da suka kira "Jarumta".

Mata dai a kasar na sanya abaya ne tare da rufe kansu da mayafi idan za su fita waje. Haka kuma an haramta musu tuka mota kuma basa cakuduwa da maza.

A bidiyon wanda da fari aka wallafa a dandalin sada zumunta na Snapchat a karshen mako, an nuna Khulood na tafiya a wani lungun da ba kowa a gidan tarihin na Ushayqir, wanda ke lardin Najd da ke da nisan kilomita 155 daga arewacin babban birnin kasar wato Riyad.

Najd na daya daga cikin wuraren da ake da tsabar riko da addini a kasar. Nan ne inda aka fara kafa izala wanda gidan sarautar kasar ke bi a karshen karni na 18.

Daga nan ne kuma bidiyon ya fara bazuwa a shafin twitter, inda aka samu banbancin ra'ayi a kansa. Inda wasu ke neman a dauki mataki a kanta, wasu kuma ke cewa a barta ta sanya abin da take so.

Wani dan jarida Khaled Zidan ya ce: "Dole a dawo da Haia [Hizbah]."

Yayin da wani kuma ya rubuta cewa: "Dole mu bi dokar kasa. A Faransa an hana sanya niqabi kuma ana cin tarar duk wata wadda ta karya dokar. A Saudiyya kuwa dokar ita ce a sanya abaya da duk wata sutura ta mutunci da ke rufe jiki."

Wani marubuci kuma masanin falsafa, Wael al-Gassim, ya ce na kadu da na ga wadanan kalaman na ban tsoro da aka bayyana ciki fushi a twitter".

"Don ni nayi tsammani ne ko ta kashe wani ne, amma sai naga ashe maganar siket din da ta sanya ake magana akai wanda basa so. Ban san yadda kasar zata yi nasarar cimma burinta na 2030 ba idan an kama ta. Yana hannunka mai sanda ga shirin yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman da aka kaddamar a bara.

Fatima al-Issa ta wallafa martani kamar haka: "Idan da ace 'yar kasar waje ce da yanzu suna yaba kyaunta da kugunta da kyawun idanunta...Amma da yake 'yar Saudiyya ce suna neman a kama ta."