Kotu ta ba da umarnin kwace kadarorin Diezani

Diezani Alison-Madueke

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana zargin Diezani da sata, zargin da ta sha musantawa

Wata babbar kotun da ke Lagos ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace kaddarorin tsohuwar ministar man Najeriya Diezani Alison-Madueke.

Rahotanni sun ce Madam Diezani ta sayi kaddarar da ke yankin Banana Island da ke Lagos a kan kudi da suka kai $37.5m.

Kaddarar dai wani rukunin gini ne mai kunshe da manyan dakuna 24, da gida 18 da gidajen zamani da ke yi a saman bene shida, a cewar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC.

Baya ga kaddarorin, alkalin kotun mai shari'a Chuka Obiozor ya ba da umarnin kwace $2,740,197.96 and N84,537,840.70, kudaden hayar gidajen da aka biya tsohuwar ministar man.

Rahotanni na cewa an gano kudin ne a ajiye a wani bankin kasuwanci na kasar.

Alkalin ya bayar da umarnin ne ranar Laraba bayan da lauyan EFCC Mr. Anselem Ozioko ya shigar da bukatar yin hakan.

Ozioko ya shaida wa kotun cewa EFCC tana zargin Diezani da yin amfani da kudin haram wurin sayen kaddarorin.

Lauyan ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa Madam Diezani ta biya $37.5m kudi-hannu wurin sayen kaddarar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka kwace kaddarorin tsohuwar ministar man.

A watan Aprilun 2016, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai N593m daga hannun tsohuwar ministar.

Ana zargin ta da sace wa da kuma yin facaka da kudin kasar a lokacin da take ministar man, ko da yake ta sha musanta zargin.

A watan Fabrairun 2017 ma, wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince a halatta tare da mallakawa gwamnatin kasar kudaden da aka samu daga wajen tsohuwar ministar man, Diezani Allison-Madueke.