Gwamnatin Nigeria ta bukaci karfafa tsaro kan rikicin Kaduna

Farfesa Osinbajo ya jajanta wa dangin mutanen da rikicin ya shafa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farfesa Osinbajo ya jajanta wa dangin mutanen da rikicin ya shafa

Mukaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ba da umarnin karfafa tsaro a jihar Kaduna sakamakon rikicin kabilanci da ya haddasa asarar rayuka a farkon wannan mako.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musammam ga mukaddashin shugaban kasar, Laolu Akande ya fitar, Farfesa Osinbajo ya jajanta wa dangin mutanen da rikicin ya shafa, kuma ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga mutanen da suka ji raunuka.

Kafofin yada labaran Nijeriya sun ambato rundunar 'yan sanda na cewa zaman lafiya ya dawo kauyukan Kajuru na jihar Kaduna, inda rikici tsakanin mutanen yankunan da Fulani ya yi sanadin mutuwar gomman mutane.

Suka ce kwamishinan 'yan sandan Kaduna, Agyole Abeh, yayin wani taron manema labarai na cewa an kashe akalla mutum 33 a hari guda biyu.

Ya ce rikicin ya faro ne a ranar 11 ga watan Yuli lokacin da mutanen wasu kauyuka suka far wa wani yaro da mahaifinsa.

Suka ce 'yan sanda sun kai dauki yankin amma matasan da ke rikicin tuni sun arce zuwa dazuka, inda suka bar mutanen da aka kashe, akasari mata da kananan yara.

Da yake yin tir da rikicin, mukaddashin shugaban Nijeriya ya nunar cewa kalubalen tsaro a Kudancin Kaduna da ya haddasa mutuwar mutane, wani babban abin damuwa ne ga gwamnatin kasar.

Ya kuma yi alkawarin tabbatar da yin adalci ga mutanen da aka kashe ko kuma aka jikkata da ma sauran wadanda rikicin ya shafa.

Labarai masu alaka