Zazzabin cizon sauro na karuwa a Nigeria —WHO

Sauro ma yada cutar zazzabi Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce sama da kashi 95 cikin dari na 'yan Nijeriya ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Cutar zazzabin cizon sauro na cikin cututtukan da ke addabar manya da yara da kan jefa masu karamin-karfi cikin halin kaka-nika-yi, inda dubban mutane kan mutu a kowace shekara.

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce sama da kashi 95 cikin dari na 'yan Nijeriya ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Ta kuma ce Najeriyar ce ke da kusan kashi 23 cikin dari na masu kamuwa da cutar a duniya , da kuma kashi daya bisa uku na wadanda cutar ta zazzabin cizon sauro ke kashewa a duniya.

Kwararru dai sun ce cutar ta fi illa ga yara wadanda ta kan hallaka idan ba a gaggauta yi musu jinya ba.

Sauro kan samu makwanci a da saurin yaduwa a manyan birane da dama a Nijeriya, ciki har da jihar Kano.

Dr Ashiru Mohammed Sumaila, likita ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, da kuma kan yi aiki a wasu kananan asibitoci a jihar, kuma ya shaida wa BBC cewa lokaci na saukar ruwan sama, ana yawan samun zazzabin cizon saura a ko ina a Nijeriya, musamman a arewa.

Ya kuma kara da cewa; '' wannna ciwo yana matukar yawa a cikin al'umma kuma ya kan taba yaro ya taba babba, sai dai ya fi illa ga yara da mata masu ciki.''

Hakkin mallakar hoto D POLAND/PATH
Image caption Cutar zazzabin cizon saura ta fi yin illa ga kananan yara da mata masu juna biyu

Ganin irin illar da ke tattare da wannan cuta gwamnatin jihar ta fara aiwatar da wani shirin yaki da cutar Maleriyar ko zazzabin ta hanyar ba da magunguna, da gidan sauro mai mmagani kyauta.

Kwamishin lafiya na jihar Dr Kabiru Ibrahim Getso ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta tanaji magani na Naira miliyan dari da tamanin da uku, da aka raba wa asibitoci guda 748.

'' Duk kuma wanda aka ga yana fama da zazzabi ma zafi a akwai wata allura da ake ba shi kyauta don ceto rayuwarsa.''

Sai dai wasu kwararru na cewa duk da tasirin da wannan shiri ke yi za a fi ganin alfanunsa idan gwamnati ta bada fifiko wajen daukar matakan riga-kafi.

Kana asarar rayukan jama'a da ake yi sakamakon zazzabin cizon sauron zai ragu sosai idan mahukunta a sauran sassan Nijeriyar suka dukufa wajen daukar matakai.

Labarai masu alaka