Kamfanin Etisalat Nigeria ya sauya suna zuwa 9Mobile

9Mobile Hakkin mallakar hoto .
Image caption Kamfanin 9Mobile na da ma'aikata sama da 4,000 a Najeriya

Kamfanin wayar sadarwa na Etisalat a Najeriya ya sauya suna zuwa 9Mobile, bayan hedikwatar kamfanin da ke Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shelar janye wa daga Najeriya.

Hukumar da ke sa ido a kan harkar sadarwa a kasar (NCC) ta bayyana amincewarta da sauya sunan a hukumance.

Kamfanin na 9Mobile ya ce duk da cewa sunansa ya sauya, nagartar aikin da ya ke wa masu hulda da shi bai sauya ba.

Kamfanin ya ce ya zabi 9Mobile ne domin ci gaba da tasirinsa na kasancewa kamfanin sadarwa na hudu mafi girma a Najeriya.

Etisalat ya janye ne daga Najeriya domin kamfanin ya kasa biyan bashin da gamayyar bankunan kasar 13 ke binsa.

Lamarin da yasa bankunan suka yi barazanar kwace Etisalat Nigeria, amma hukumar NCC da babban bankin Najeriya suka shiga tsakani domin kare ayyukan mutane fiye da 4,000 da kuma harkar kudin Najeriya.

Eitsalat ta janye jarinta daga reshenta na Najeriya ne kamfanin ya shiga rikici da bankunan.

Sai dai Hukumar NCC da babban bankin Najeriyar sun dauki matakan sake fasalin kamfanin.

Labarai masu alaka