India: An hana zubar da cikin yarinya mai shekara 10

Indiya zubar da ciki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Indiya zubar da ciki

Wata kotu da ke kasar Indiya ta hana a zubar da cikin wata yarinya mai shekara 10 wadda ta samu ciki bayan an yi mata fyade.

Cikin yarinyar ya kai kimanin wata shida kuma ana zargin kawunta ne ya yi mata cikin bayan ya yi mata fyade.

Likitoci sun bai wa kotun da ke Chandigarh a Punjab shawarar ka da a zubar da cikin domin hakan zai jefa rayuwar yarinyar cikin hadari.

Sai dai kuma har ila yau ana fargabar yadda yarinyar za ta yi goyon cikin har zuwa haihuwa da kuma yadda hakan zai shafi lafiyarta.

A watan Mayun da ya gabata ma dai wata kotu da ke Harnaya ta sa an zubar da cikin wata yarinya, wadda ita ma shekararta 10 a lokacin da take da cikin wata biyar.

Ana zargin mijin mahaifiyar yarinyar ne ya yi mata fyade.

Fyade dai na ci gaba da zama wata babbar matsala a kasar, inda dubban mutane suka yi zanga-zangar matsin lamba a kan gwamnati da dauki matakan dakile matsalar.