Nigeria: 'Direbobi sun kona bankin Diamond a Lagos'

'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zuwa yanzu hukumar 'yan sanda ba ta ce komai ba

Rahotanni daga birnin Lagos sun ce wani dan sanda da ke gadin bankin Diamond a unguwar Apapa, ya harbi wani direban motar haya.

A take dai wanda aka harba din ya mutu.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa hakan ya sa rayukan mutanen da ke wajen musamman sauran direbobi suka baci suka yi kan 'yan sandan da ke gadin bankin, inda su kuma suka ruga cikin bankin don neman mafaka.

Wani ganau ya ce ganin hakan ya sa sauran direbobin suka cinnawa bankin wuta.

"Tuni aka turo 'yan sandan kwantar da tarzoma wajen, har ma kuma sun kama wasu mutane sun yi gaba da su," in ji mutumin wanda ba ya so a ambaci sunansa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar ya shaida wa BBC cewa sun shawo kan lamarin, kuma an mayar da doka da oda.

Ya kara da cewa jami'ansu sun kama wasu matasa da suke zargi da hannu wurin tayar da yamutsin.

Wajen da ala'marin ya faru dai wuri ne na hada-hadar jama'a sosai, ana kuma yawan yin dakon mai a manyan motoci.

A yanzu dai hatsaniyar ta lafa amma 'yan sanda na ci gaba da sintirin a yanki.

Zuwa yanzu dai ba a san irin barnar da wutar da aka cinnawa bankin ta jawo ba.

A Najeriya dai ana yawan samun irin wadannan rigingimu inda wasu lokutan jami'an tsaro ke kashe mutane ba bisa ka'ida ba su kuma 'yan kasa suke daukar doka a hannunsu.

Labarai masu alaka