Zimbabwe: Zaki ya kashe yarinya 'yar shekara 10

A lioness lays down in Zimbabwe's Hwange National Park (November 2012). Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption The attack is believed to have happened near a game reserve

Zaki ya hallaka wata yarinya a yayin da ta fita yin fitsari da daddare a bayan bukkarsu da ke wani kauye a Zimbabwe.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan kasar ne ya shaidawa wata jaridar kasar faruwar lamarin.

Wani mataimakin sifeton 'yan sanda Kudakwashe Dehwathe ya ce, kanwar mahaifiyar yarinyar mai suna Mitchell Mucheni, ta ce ta ga lokacin da zakin ke jan yarinyar zuwa cikin daji.

Ya kara da cewa, daga baya an samo gawar yarinyar a nisan mita 300 daga kauyen.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddarea Chiredzi.

Ana yawan yin fada tsakanin mutane da dabbobi a yankunan da ke kudu maso gabashin Zimbabwe.

A watan da ya gabata, sarkin Maranda da ke kusa da Mwenezi ya roki hukumar kula da gandun namun daji ta kasa da su taimaka musu bayan da zakuna suka gallabe su da kashe wa mutanen kauyukan dabbobi.

Zimbabwe Parks and Wildlife Management Authorities (ZimParks) has yet to comment on this latest case.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC