Maza sun fi mata yawan albashi a tsakanin shahararrun ma'aikatan BBC

Claudia Winkleman da Alex Jones Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Claudia Winkleman da Alex Jones su ne matan da BBC tafi biya albashi mafi tsoka

Hukumar gudanawar BBC ta bayyana cewa kashi biyu cikin uku na shahararrun ma'aikatanta masu karabar albashin da ya gota fam 150,000 maza ne, kuma Chris Evans shi ne na farko a inda ya ke samun daga fam miliyan 2.2 zuwa 2.25 a shekara.

Claudia Winkelman ce mace mafi yawan albashi, inda ita kuma ta karbi albashi tsakanin fam 450,000 zuwa fam 500,000 a bara, in ji BBC a cikin bayanan kudaden da ta kashe a shekarar 2016/2017.

Alex Jones mai gabatar da shirin 'The One Show', shi ne na biyu, inda ya ke karbar fam 450,000 zuwa fam 500,000.

Shugaban BBC Tony Hall ya ce akwai sauran aiki a gaba wajen daidaita albashin maza da mata.

Cikin shahararrun ma'aikatan na BBC 96 mafi yawan albashi, bakwai na farko duka maza ne.

Wannan shi ne karo na farko da a ka bayyana yawan albashin da BBC ta ke biyan shahararun ma'aikatanta.

An tilasta wa BBC yin haka ne bayan da a ka yi wa dokar da ta kafa BBC gyara.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wannan bambancin albashin na iya zama matsala ga BBC

A lokacin da ta ke magana a tashar Rediyon LBC, firai ministar Burtaniya, Theresa May ta ce: "Mun ga yadda BBC ta ke biyan mata albashin da bai kai na maza ba, bayan kuma aiki iri daya suke yi... Ina son a rika biyan mata albashi daidai da na maza."

Da a ka tambayeta ko wannan na nufin Chris Evans ya fi ta daraja kenan, sai ta ce: "Abu mafi muhuimmanci shi ne yadda BBC ke biyan maza da mata albashi daban bayan ko aiki iri daya su ke yi."

Yawan kudin da a ke biyan shahararrun ma'aikata 96 na farko ya kai fam miliyan 28.7, amma alkaluman da ke cikin rahoton sun nuna wani wagegen bambancin albashi tsakanin maza da mata.

"A bangaren kawo daidaito a wajen aiki, BBC ta fi kafofin watsa labarai da sauran ma'aikatun gwamnati masu yawa nuna adalci", in ji Lord Hall.

"Muna samun ci gaba sosai, amma kuma mun yarda cewa akwai sauran aiki a gaba, sannan muna kan gaba wajen cimma muradun kawo daidaito fiye da sauran kafofin watsa labarai."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
"Akwai sauran aiki a gaba" wajen rufe wagegen gibin albashi in ji shugaban sashin rediyo da Ilimi na BBC

Da a ka tambayi Lord Hall idan wannan lamarin na nufin cewa shahrarrun matan da ke yi wa BBC aiki zasu fito karara su bukaci karin albashi, sai ya ce, "Zamu cigaba da aiki tare da shahararrun ma'aikatanmu cikin natsuwa."

Ita kuwa kungiyar kwadagao ta Equity cewa ta yi: " Wannan bambancin tsakanin albashin da a ke biyan maza da mata da bakar fata da 'yan asalin yankin Asiya da ma 'yan tsiraru abin damuwa ne."

Mai gabatar da shirin 'Woman's Hour', Jane Garvey shiga Twitter tayi inda ta ce: "Ina murnar fara gabatar da shirin @BBCWomansHour na yau. Kuma zamu tattauna bambancin albashin maza da mata kamar yadda muke yi tun 1946. Da alama komai na tafiya daidai ko?"

Ita ma Emily Maittlis mai gabatar da shirin Newsnight ta sake tura sakon Garvey a Twitter watau ta mara wa matakin da ta dauka kenan.

Wani mai gabatar da shirin 'Today' a tashar Radio 4, John Humphrys ya yarda cewa zai yi wuya a fahimci cewa albashinsa na fam 600,000 bai yi yawa ba: "Idan a ka duba, babu yadda zan iya kare kaina game da wadannan kudaden masu yawa, idan ka kwatanta ni da wasu."

"Idan likita ya ceto rayuwar wani yaro, ko wata malamar jinya ta nuna wa wani maras lafiya kulawa, ko wani mai kashe gobara ya auka cikin dogon benen Grenfell, to kana iya cewa ban cancanci karbar irin kudin da nake samu ba. Amma gaskiyar lamarin shi ne, harkar ta kasuwanci ce."

Image caption Manyan shararrun ma'aikatan BBC da yawan albashin da suke karba

A daya bangaren kuma, akwai bambanci tsakanin shahararrun ma'aikata farar fata da ma'aikata bakar fata da ma mutane 'yan asalin nahiyar Asiya.

George Alagiah, da Jason Mohammad da Trevor Nelson sune masu albashi mafi tsoka wadanda ba fara fata ne ba. Kuma kowannensu na karbar kasa da fam 300,000.

A cikin wadanda ba turawa ne ba, Mishal Hussain ce macen da tafi kowace ma'aikaciyar BBC karbar albashi mai tsoka, inda a ke biyanta tsakanin kimanin fam 250,000.

Karin bayani

Labaran BBC