'Na yi takaicin rashin zuwa gasar Paralympics' - Lauritta

Gold medalist Lauritta Onye of Nigeria Rio 2016 Paralympic Games at the Olympic Stadium on September 11, 2016 in Rio de Janeiro, Brazil. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lauritta Onye (A tsakiya) ta Najeriya wacce ta ci lambar zinare a wasannin nakasassu na Rio 2016 a kasar Brazil tare da Rima Abdelli ta Tunisia da Lara Baars ta Holland.

'Yar Najeriyar nan mai rike da kambun gasar wasannin nakasassu, wadda kuma ta kafa tarihi a duniya, Lauritta Onye ta bayyana takaicinta dangane da abun da ya hana ta halartar gasar wasannin nakasassu da ke gudana a birnin Landon.

"Rai na ya yi matukar baci sosai a kan lamarin, kasancewa ina kallon gasar ne kawai a talabijin, a matsayina na gwarzuwar duniya dake cikin bacin rai", in ji Lauritta.

Lauritta ta koka da yadda gwamnati ta kyale su babu bayani, "Babu wani labari da muke ji tun bayan da muka yi wasannin gwaji watanni biyu da suka wuce. Ba mu ji komai ba daga ma'aikatar wasani ba har yau".

Gwamnatin Nigeria ta kare kanta daga zargin rashin kulawa da cigaban wasannin nakasassu a kasar.

"Harkar wasa a na yi ne da kungiyoyi, ba da gwamnati ba. Kungiyoyin ne ke da dangantaka da uwar kungiya ta duniya dake shirya wasannin Paralympics", in ji Barister Solomon Dalong, ministan wasanni da harkokin matasa na Najeriya.

A shekarun baya 'yan wasan Najeriya sun wakilci kasar a wasannin Paralympics, kuma har sun ciyo wa kasar lambobin yabo.

Ministan ya kare gwamnati daga zargin rashin shiryawa gasar, "Maganar ita ce, shin mun cancanci mu kasance a wajen gasar?"

Ya kara da cewa, "Idan mun cancanta amma ba mu je ba, to shi ne zamu yi takaici."

Wasannin na bana da a ka lakaba wa sunan London 2017, su ne na takwas a jerin gasar da kasashe daban-daban suka dauki nauyi gabatarwa.

Kasar Qatar ce ta dauki nauyi gasar da a ka yi a watan Oktobar 2015, inda 'yan wasa 1,229 daga kasashe 90 suka halarci wasannin.

A wancan lokacin, kasar Sin ce ta daya da lambar girma 85, wadanda a ciki 41 na zinare ne.

Labarai masu alaka