'Za mu ceto da matan da BH ta sace'

Farfesa Yemi Osibanjo
Image caption Tun daga shekarar 2009 ne mayakan Boko Haram suka zafafa kai hare-hare a yankunan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya

Mukaddashin shugaban Najeriya farfesa Yemi Osibanjo, ya yi Allawadai da sace wasu mata da ke cikin ayarin masu raka gawar wata 'yar sanda da mayakan Boko Haram suka yi, a kan hanyar garin Damboa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da ofishin mukaddashin shugaban ya fitar, Osibanjo ya ce ya na jajantawa 'yan uwan matan goma da aka sace, tare da alkawarin gwamnati za ta yi kokarin ganin an kubutar da su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mukaddashin shugaban kasar ya umarci rundunar sojin Najeriya da hukumomin leken asiri da taimakon hukumomin tsaro na kasashenn waje da ke taimakawa Najeriya a yakin da ta ke yi da kungiyar Boko Haram, su dauki dukkan matakan da suka kamata dan kubuto da matan.

Osibanjo ya kuma ce za a kara daukar matakan tsaro a a ciki da wajen jihar Borno musamman kauyuka da 'yan BH suka fi kaddamar da ayyukansu.

Lamarin dai ya faru ne tun ranar 20 ga watan jiya,a lokacin da suke kan hanyar raka gawar wata 'yar usarsu 'yar sanda da ta mutu, amma sai a farkon makon nan kungiyar BH din ta haska matan a bidiyon,

Tun da fari rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce matan da aka sace ba jami'anta ba ne, wadda ta rasu ce kadai ma'aikaciyarsu. Sanarwar na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 da kiraye-kirayen 'yan uwan matan suka yi a wata hira da BBC a safiyar jiya laraba.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun ce ya kamata hukumomi su fito su bayyana gaskiyar al'amarin batun sace mata da mayakan Boko Haram suka yi.

Wasu na ganin cewa rashin bayyana ainahin gaskiyar abinda ya faru da amincewar tabbas an sace 'yan matan Chibok da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta yi, ya kara janyo matsalar da har yanzu ba a kubuto da sauran 'yan matan ba.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari dai ta hau mulki ne da shan alwashi hadi da yi wa 'yan Najeriya alkawarin magance matsalar tsaro da ke addabar kasar musamman yankin arewa maso gabas.

Labarai masu alaka