Amnesty: Kamaru na azabtar da 'yan BH da take tsare da su

Boko Haram
Image caption Amnesty ta ce, babu wata kwakkwarar shaida da jami'an tsaron Kamaru su ke da ita, da za ta tabbatar mutanen da ake tsare da 'yan boko haram ne

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce jami'an tsaron Kamaru, suna azabtar wa da hallaka wadanda ake zargin 'yan kungiyar Booko Haram ne da ake tsare da su tun a shekarar 2013.

A wani rahoto da Amnesty mai mazauni a Birtaniya ta fitar, ta ce an gabatarwa gwamnatin jamhuriyar Kamaru shaidun da suka nuna an aikata hakan amma kawo yanzu babu wani martani da gwamnatin ta maida.

Kungiyar ta ce jami'an tsaron Kamaru na tsare da daruruwan wadanda ake zargin da hannu a kungiyar Boko Haram, ba tare da gabatar da wata shaida sahihiya da ta nuna su na cikin kungiyar ba.

Yawancinsu dai matasa ne daga shekara 15 zuwa magidanta 'yan shekara 45, amma a halin da ake ciki har da mata da kananan yara a cikin wadanda ake tsare da su din.

Haka kuma ana azabtar da mutanen ta hanyar ba su horo da suka hada da sheka musu ruwan sanyi, ko sanyawa su tsaya a lankwashe na tsahon lokaci.

Binciken da Amnesty ta gudanar, ta samu shaidun gani da ido da suka tabbatar da mutuwar yawancin mutanen saboda tsananin azaba a hannun jami'an Kamarun, kuma ba lallai ne a samu kiyasin ainahin adadin wadanda suka mutu ba.

Ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram, sun daidaita yankin arewacin Kamaru mai iyaka da arewacin Najeriya, da wasu yankunan kasashen Chadi da jamhuriyar Nijar.

Rahoton Amnesty ya zargi sojojin kasar Faransa da Amurka na yankunan dan taimakawa kasashen yaki da 'yan ta'addar, kuma kusan sun san halin da ake ciki na azabtar da wadanda ake zargin amma ba su taba daukar wani mataki akai ba.

To sai dai kuma, babu wata shaida da aka samu da ta nuna akwai sa hannun dakarun kasashen waje a yiwa mutanen izaya.

Sai dai karshen rahoton kungiyar, ya bukaci gwamnatocin kasashen su gudanar da bincike, ko sojojin wanzar da zaman lafiya sun san abinda ke faruwa amma suka ki daukar mataki akai.

Labarai masu alaka