An kama wani yariman Saudiyya kan cin zarafi

Sarki Salman ya ce dole a dauki hukunci kan duk wanda ya keta doka komai matsayinsa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sarki Salman ya ce dole a dauki hukunci kan duk wanda ya keta doka komai matsayinsa

An kama wani yariman Saudiyya kan zargin da aka yi masa na kasancewar hannunsa a wani lamarin cin zarafin dan adam da aka nada a faifan bidiyo.

Sarki Salman ya bayar da umurnin a kama shi nan take bayan bidiyon ya bayyana a Intanet kuma ya bazu, lamarin da ya sa ya zama abin da aka fi magana a kai a shafukan Intanet na kasashen Labarawa.

An kwarmata bidiyon kama matashin yariman, mai dogon bakin gashi da bakar riga a Intanet, inda aka yi ta yayatawa tare murna a kafofin sada zumunta na Saudiyya.

Umarnin sarkin ya tabbatar da cewar za a dauki matakai domin hana tilastawa tare da cin zarafin mutane komai matsayin mutum.

Karanta labarai masu alaka:

Labarai masu alaka