Aku ya bayar da shaida kan matar da ta kashe mijinta

Glenna and Martin Duram pictured Hakkin mallakar hoto ABC
Image caption An samu Glenna Duram da laifin kashe mijinta Martin

An samu wata mata da laifin kashe mijinta bayan ta harbe shi sau biyar a wata shari'ar kisan kai a Michigan ɗin Amurka, wadda bisa dukkan alamu wani aku ya shaida.

Glenna Duram ta kashe mijinta, Martin, a gaban tsuntsun gidan a shekarar 2015, kafin ta juya bingidar tana yunkurin harbe kanta ko da yake, hakan bai yi nasara ba.

Daga baya dai akun ya yi ta nanata furucin "kar ki harba!" yana maimaita kalaman mamacin, in ji tsohuwar matar Mista Duram.

Ba a dai yi amfani da akun, wanda nau'in na Afirka ne mai launin toka da ake kira Bud, wajen ba da shaida a cikin kotu ba.

Masu taya alƙali shari'ah sun samu Misis Duram, mai shekara 49, da aikata babban laifin kisan kai. Ko da yake, sai a watan gobe ne za a yanke mata hukunci.

Lamarin wanda ya faru a gidansu da ke Sand Lake cikin watan Mayun shekarar 2015, ya sa ta jin ciwo a ka amma dai Allah ya yi da sauran kwananta a gaba.

Mahaifiyar mamacin, Lillian, ta ce "abin damuwa" ne ganin wadda ta yi kisan Misis Duram na nuna halin ko-in-kula a kotu lokacin da aka gabatar mata da hujjoji kan abin da ta aikata.

Ta ce: "Hakan bai kamata ba; bai kamata ba ne kawai. Shekara biyu ya yi tsawo wajen jiran adalci."

Image caption Bisa ga dukkan alamu, Bud, aku mai ruwan toka daga nahiyar Afirka, kamar wanda ke cikin hoton nan , na da baki "mafi datti"

Tsohuwar matar Mista Duram, Christina Keller, wadda ta mallaki Bud yanzu, ta ce ta yi imanin cewar akun yana maimaita maganar da ya ji cikin daren da aka yi kisan ne, da ta ce ya ƙare da kalaman "kar ki harba!", tare da wata kalmar zagi.

Iyayen Mista Duram sun yarda cewar mai yiwuwa ne tsuntsun ya ji ce-ce-ku-cen da ma-auratan ke yi kuma yana maimaita kalamansu na ƙarshe.

A lokacin mahaifin Mista Duram ya shaida wa kafafan yada labaran yankin cewar:"A ganina tsuntsun yana wurin, ya tuna kalaman, kuma yana furta su."

Mahaifiyarsa, Lillian Duram, ta kara da cewar : "Wannan tsuntsun yana naɗar komai-da-komai, kuma ya fi kowanne tsuntsu baki mai datti."

Daga farko wani mai gabatar da kara a Michigan ya yi tunanin amfani da muryar akun a matsayin hujja a shari'ar kisan, amman an yi watsi da wannan daga baya.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC