Atiku 'na so talakawa su karbi mulki'

Atiku da Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Atiku ya fafata da Buhari a zaben fitar da gwani na shugabancin Najeriya a APC

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce yana so a sake fasalin kasar yadda talakawa za su karbi ragamar tafiyar da ita.

A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon dan takarar shugaban Najeriya ya ce, "ina so a sauya tsarin kasarmu domin kwace mulki daga masu kudi zuwa mutanen da suka mallake ta {talakawa}".

"Babban makasudin sake fasalin kasar shi ne a kawar da tsare-tsaren da suka fifita wasu kan wasu wajen rabon arziki. Ana bayar da arzikinmu ga wasu mutane kalilan maimakon a bayar ga dukkanmu. Don haka ya kamata a kawo karshen hakan," in ji tsohon gwamnan jihar Adamawa.

Sai dai ya ce sake fasalin kasar ba zai zama sha yanzu magani yanzu ba, yana mai cewa, "mutanen da ke son raba kawunan 'yan kasar nan na ganin da zarar sun cimma burinsu za su rika rayuwa kamar a aljanna. Amma ba haka batun yake ba".

Batun sake fasalin Najeriya dai ya sake tasowa ne tun bayan da masu fafutikar kafa kasar Biafra sun soma neman tsaga Najeriya.