Jami'an tsaron Nigeria suna mana shisshigi — DSS

Nigeria Police

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zargin jam'ian tsaro a Najeriya da wuce gona da irin wajen gudanar da aikinsu

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta gargadi hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci da rashawa da su daina amfani da sunanta wajen aiwatar da ayyukan da suka saba wa doka a sassan kasar.

Wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta DSS, Tony Opuiyo, ya fitar, ta ce wani lokacin jami'an tsaron su kan kwaikwayi irin kayan aikinsu da kuma yadda hukumar DSS take gudanar da aikinta.

Hukumar ta ce masu yin wannan aikin na neman a yarda da aikinsu ne, tana mai bayar da misali da samamen da aka kai gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, a Kaduna.

Sanarwar ta kuma ce ba ita ta kai samamen da aka kai wani ofishin kamfanin makamashi na Sahara Energy Company a Abuja ba.

Saboda haka hukumar ta ce ya kamata mutane su gane cewar ba dukkan jami'an tsaro masu sanye da bakaken kaya ne jami'ansu ba.

Hukumar ta ce tana iya kokarinta na kawo karshen wannan dabi'ar, tana mai karawa da cewar za ta ci gaba da bayyana wa masu ruwa da tsaki abubuwan da ke tafe a ayyukanta.

Ta kuma nemi mutane da ke da bayanai game ayyukan da ake zargin cewar ana yin su ba bisa ka'aida ba, da su tsegunta mata lamarin.

An dade ana sa-in-sa tsakanin hukumomin tsaro a Njeriya, amman ba safai yake fitowa fili irin wannan ba.