Yadda Kasuwar sha ka fashe ke habaka a Sudan

A jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, Yousra Elbagir ta yi nazari kan yadda wasu matan Sudan ke komawa amfani da magungunan kasuwannin bayan fage a kokarinsu na kara kyau.

Two plastic bottles containing small pink and white pills.

Asalin hoton, Yousra Elbagir/BBC

Bayanan hoto,

Ana iya samun magungunan kiba da ke da illa a wurin masu talla ba bisa ka'ida ba

Yayin da aka dade ana amfani da mayukan shafe-shafe a fadin Sudan don kara hasken fata, wani sabon yayin kuma na ci gaba da bazuwa a kasar.

Matasa da dama sun koma amfani da kwayoyin sa kiba, da fatan zama sambala-sambalan matan da suke gani a matsayin cikar kyau.

Sabanin ka'idar kwararrun masu hada magunguna, kananan shagunan da ke sayar da mayukan bilicin da sauran kayan kara hasken fata, suna bayar da magungunan sha-ka-fashe ta hanyar da ta saba ka'ida.

Magungunan da ake sayar wa daidaiku, a cikin 'yan jakunkuna da mazuban alawa, ba kuma tare da duk wani bayani game da hatsarinsu ga lafiya ba.

Abin boye ya fito fili

Abu ne mai wuya a ce ga adadin matan Sudan da ke amfani da wadannan kwayoyi na sha-ka-fashe, don kuwa da yawa ba sa yarda a san suna sha.

"Ana sayar da su ne a hannu cikin kauyuka kamar alewa," a cewar Imitithal Ahmed, wata daliba a Jami'ar Khartoum.

"Ina tsoron yin amfani da su saboda na ga 'yan'uwana sun kamu da rashin lafiya."

'Sa Uwa Zargi'

Sau da yawa ana sabunta wa magungunan sunaye, inda ake ba su suna mai daukar hankali don fito da tasirinsu.

Kama daga Sanya makwabta mamaki da Cikar Kaji zuwa su Sanya Uwa Zargi, ana mantawa da sunayen kwayoyin na asali tare da maye gurbinsu da alkawurran manyan mazaunai da sambala-sambalan cinyoyi da ciki mul-mul wanda har iyaye za su rika tunanin ko an samu juna-biyu.

Shugaban kungiyar kwararrun masu hada magunguna a Sudan, Dr. Salah Ibrahim ya ce amfani da wasu nau'in magungunan sha-ka-fashe masu sinadaran steroids ba tare da kulawar likita ba ka iya yin illa ga zuciya da hanta da koda da makoshi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

"Yawancin matan Sudan suna da kiba kuma suna da haske"

Mummunar illa

Mata matasa a Sudan na mutuwa sakamakon ciwon koda da na zuciya, wadanda akan samu saboda daukewar sinadaran steroid a cewar kwararru.

Amare musammam sun fi zama ruwan dare a cikin mamatan, bayan sun shafe tsawon wata guda suna kwalliyar gyaran jiki kafin ranar aurensu, daga nan kuma sai kwatsam su daina amfani da magungunan sha-ka-fashe da mayukan bilicin.

Amma duk da haka, wannan yayin mai tsoratarwa na ci gaba da samun karbuwa.

Daliban Jami'a sukan yi dandazo wajen sayen wani maganin kashe ciwo Tramadol, da ake sayar da kwaya daya a kan fam 20 ta Sudan.

An san wasu masu sayar da shayi a gefen titunan birnin Khartoum da ke jefa irin wannan kwaya a kofin shayi, bayan mai bukata ya yi musu wani zaurance.

Gangamin wayar da kai ya zuwa yanzu bai yi wani tasirin a-zo-a-gani ba.

Asalin hoton, YouTube

Bayanan hoto,

Da yawa daga cikin matan Sudan suna ganin Nada Algalaa a matsayin wata wadda ta fi dacewa da surar mace a kasar

Dr Ibrahim, shugaban kungiyar kwararrun masu hada magunguna, ya bayyana karo da dama a kafar talbijin ta kasar, inda yake gargadi game da illolin yin amfani da magunguna ba bisa ka'ida ba.

Sudan ba ita ce al'ummar kadai da ke kallon kiba a matsayin wani wata alamar samun daukaka da iko, abin da 'yan mata ke bugun kirji da shi don nuna cewa sun "isa aure".

Amma a wannan kasa, hakan na nuna wata kima mafi dacewa.

Tana fayyace cikar mace Sudaniya - mai jiki da haske - abin da ke fito da kyawu da fasalin matar da kowa ke kulafuci.