Girgizar kasa ta kashe mutane a Turkiya da Girka

Turkiyya da Girka na makwabtaka

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Zurfin girgizar ya kai kilomita 12 a kasa

Akalla mutane biyu ne suka mutu sannan wasu gommai sun jikkata sakamakon wata girgizar kasa wadda ta shafi wasu manyan wuraren shakatawa na Turkiya da Girka da ke bakin ruwan Aegian Sea.

Girgizar kasar dai ta faru ne da misalin karfe 10:30 agogon GMT.

Kasa ta dare tsayin kilomita kusan goma a yankin Bodrum sannan kuma ta yi tafiyar kilimitar goma a gabashin Kos.

Mutanen biyun sun mutu ne a bangaren tsibirin Kos da ke yankin Girka lokacin da rufin wani gini ya rufta.

An kuma samu wani dan kwarya-kwaryar ambaliyar ruwa wadda ta yi torokon da ya kai tsayin centimita 25 a yankin Bodrum na Turkiyya.