An yi garanbawul a dokokin tsaro na masarautar Saudiyya

King Salman. File photo

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A watan Janairun 2015 ne Sarki Salman ya zama sarkin Saudiyya

An samar da wasu jerin dokoki masu neman yi wa masarautar kasar Saudiyya garanbawul.

Dokokin dai za su shafi jami'an tsaron kasar da ke yakar ta'addanci da wasu batutuwa da a baya suke karkashin kulawar ma'aikatar cikin gida.

Sauran abubuwan su ne sauya shugaban dogarai na masarautar, a inda kuma aka ce an yi wasu nade-nade masu tallafa wa sabon yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman.

A watan da ya gabata ne dai aka nada yariman mai shekara 31 a wani yanayi da wasu ke ganin na son zuciya ne.

Ya maye gurbin Mohammed bin Nayef, mai shekara 57, wanda kuma yi yi mubaya ga sabon yariman.

A ranar ALhamis ne aka sanar da sabbin sauye-sauyen, wanda kamfanin dillancin labarai na kasar ya wallafa.

Ya ce an dauki matakan ne a kokarin ciyar da kasar gaba

Asalin hoton, AFP

A yanzu haka Abdulaziz bin Mohammed al-Howairini, ne sabon shugaban hukumar tsaron wanda zai yi aiki kai tsaye karkashin Sarki Salman.

Sabon shugaban dogaran masarautar kuwa shi ne Suheil al-Mutiri, wanda zai maye gurbin Hamad al-Awhaly.

Bayanan bidiyo,

Mohammed bin Nayef daga dama yana yin mubaya'a ga Mohammed bin Salman daga hagu, wanda ya durkusa yana sumbatar hannun yayan nasa dan baffansa