'Gwamnati ce ta jawo ambaliyar ruwa a Lagos'

Lagos Flood

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ambaliyar ruwa ta hana mutane sake a wasu unguwanni a Legas

Masana a Legas da ke kudancin Najeriya na cewa gwamnatin jihar na da hannu kan ambaliyar ruwan saman da jihar ta fuskanta sakamakon tunkuda ruwan tekun baya, saboda shirin da take yi na gina manyan gidaje a yankunan da aka janye ruwan tekun.

Unguwannin Victoria Island da Lekki da Aja da kuma Ikoyi su ne manya da ake ji da su a Ikko, wadanda yawanci manyan masu kudi da jiga-jigan gwamnati ke zama a can kuma suke alfahari da su.

Sai dai kuma babban abin barazana na farko ga wadannan yankuna shi ne suna dab da gabar teku.

Baya ga haka ruwan saman da ake tafkawa ya zama babbar barazana ga makomar unguwanni masu alfarma a Legas din da mazauna unguwannin.

A baya-bayan nan an shafe kwanaki kusan bakwai a jere ana zabga ruwa babu kakkautawa, lamarin da ya janyo amabiliyar da ta hana dubban ma'aikata zuwa aiki.

Bayanan hoto,

Toshewar magudanan ruwa na cikin muhimman dalilan da suka sa aka yi ambaliya a Legas

Wakilin Sashen Hausa na BBC a Legas, Umar Shehu Elleman ya ce da yawan magudanan ruwan da ke unguwanni kanana ne kuma ba za su wadatar da kwararar ruwa ba idan aka yi la'akari da cewar unguwannin na kusa da teku.

A daidai lokacin da ake ci gaba da fitar da magudanan ruwa domin samar wa ruwa hanya, BBC ta zanta da mazauna unguwannin Victoria Island da Aja domin sanin sanin yadda lamarin ya shafe su.

"Ruwa fa mun sha. Sai dai mu ce Alhamdulillahi. Don inda muke nan a tsayen nan ruwa har iya gwiwrnmu. Kuma duk kasuwanci suka tsaya. Abubuwa suka tsattsaya," in ji Danladi Dahiru Zage.

Da wakilin BBC ya tambayi mazaunin Legas din me ya sa ya ce ruwa ya shiga Eko Hotel duk da ingancin ginin otal din, sai ya ce: "Ai ba Eko Hotel ba kadai, daga nan har Aja ko ina ruwa ne."

Danladi Dahiru Zage ya ce rashin kyawun hanya ne ya jawo matsalar.

Wasu mazauna Legas din sun ce tunkunda ruwan tekun da ake yi domin gina gidaje ne silar ambaliyar, yayin da wasu ke ce wa magudanan ne suka yi karanci.

Kwararru a kan yanayi da muhallin irin su Alhassan Ahmad ABK na ganin baya ga sauyin yanayi da ke haifar da ambaliyar teku da kuma saukar ruwan sama, akwai laifin hukumomi.

Alhassan ABK ya ce: "To masu hasashe wadanda suke duba yanayi na kasa sun yi ittifakin cewar garuruwa wadanda suke kusa da teku, ciki har da Legas da Bayelsa, a shekaru masu zuwa, kamar shekara 30 zuwa 50 ko 60 akwai yanayi da zai iya faruwa amabliya ya cinye wadannan wuraren."

Bayanan hoto,

Karancin magudanan ruwa na cikin matsalolin da suke janyo ambaliyar ruwa a Legas

Ya kara da cewar: "Ainihin hanyoyin ruwan duk sun toshe, na farko kenan. Na biyu kuma ka je ka duba abun da ake yi a cikin tekun Legas. Otal fa ake ginawa, an ce za a yi kasuwa, za a yi abubuwa da yawa.

"Ruwan nan fa kara tura shi ake yi. Kuma ka fa san ruwa ko ba jima ko ba dade, shekarunsa in ya yi zai nemi hanyar wucewa ne ya wuce."

Ya kara da cewar rashin tanadin magudanar ruwa inda ruwan zai bi shi yake sa ake samun ambaliyar ruwa a tekun.

Gwamnatin jihar Legas ta hannun babban sakatare kan harkokin ruwa, Arctitech Abdullahi Kabir Ahmad ya ce gwamnatinsu tana sane da barazanar kuma ta fara magance wadannan matsaloli.

Ya ce: "Ai maganar hasashe ka gane wannan wani abu ne alkaluman kimiyya ke fada, ai duniyar ma anan gaba tashi za ta yi. Amma a yanzu ana daukar matakai daban-daban domin gujewa afkuwar hakan wato na ambaliyar ruwa a jihar Legas."

Ya kara da cewar: "Kamar misali ana sabunta magudanan ruwa a wurare daban-daban ana kuma gina sabbi. Ayyuka ne da ake ci gaba da yinsu."

Wakilin BBC ya ce a baya dai an shefe shekaru wadannan unguwanni na fama da ambaliyar ruwan teku da ruwan sama da ke malalowa, amman a sakamakon wani gyara na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da ta jihar Legas aka samu aka kange ruwan da manyan duwatsu, wani al'amarin da ya kawo karshen malalar ruwa a gaban titin Ahmadu Bello.