Me zai sa budurwa shan kayan mata?

Bayanan sauti

Adikon Zamani kan kayan mata kashi na biyu

Akwai ci gaban cikakkiyar zantawar da Fatima Zarah Umar ta fara da wasu mata game da tasirin kayan mata a makon da ya gabata, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

A cewar Hajiya Binta, wata mai sayar da kayan mata, ta ce akwai matukar amfani tattare da wadannan magunguna .... inda daya daga cikin amfaninsu shi ne kare mata daga kamuwa da cututtuka. Ita a ganinta ma, ba za kai cikakkiyar mace ba in har ba kya amfani da su.

Tana ganin dole mace ta kasance mai daddadan dandano don jawo hankalin mijinta a yayin auratayya.

"Mace ba za ta taba jin dadi da morar aurenta ba in har ba ta gamsar da mijinta," a cewar Hajiya Binta.

To wai mene ne ma ainihin amfanin kayan matan? Daga tattaunawar da na yi da kwararru, na gano wasu abubuwa kamar haka:

Na farko, yana tayar da sha'awar mace ya kuma ba ta damar gamsar da mijinta a shimfida. A ganin masu hakan na taimakawa wajen zaunar da su daram a gidajen aurensu. Mata da yawa na ganin hanyar kadai da za su bi su ji dadin aurensu ita ce su kanainaye mazajensu sai yadda suka yi da su.

Wasu suna ganin a duk lokacin da ki ka samu rashin jituwa da mijinki, to kayan mata ne za su dawo maki da zaman lafiya a cikin aurenki. Wata mata ta taba shaida min cewa, "kayan mata sun ceci aurena daga lalacewa.

Na tabbata mata da yawa na ganin haka abin yake.

Bayanan hoto,

An tafka muhawara kan batun a shafin BBC Hausa Facebook

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Haka kuma, suna ganin idan har aka yi dace ki ka iya gamsar da mijinki a shimfida to zai kara sonki kamar ya bauta maki. A ganin masu sayar da wadannan kaya, idan har ki ka iya gamsar da mijinki to kakarki ta yanke saka don zai yi komai don ki ji dadi.

A don haka suke cewa, idan har kina son zama sarauniya ko zinariya a wajen mijinki, to dole ki dinga amfani da kayan mata na sha da na sakawa irin su, tsimi, mace mai daraja, sa kishiya tagumi, da sauransu don daga darajarki.

Me zai sa budurwa ta sha?

Tambayar kenan da na yi wa masu sayar da kayan matan. Sai suka ce min ai ko kana da kyau dole ka kara da wanka, don kuwa ko kogi bai ki yayyafi ba, wato ko ke budurwa ce a ganinsu sai kin hada da gyare-gyare a lokacin aure.

To yanzu tun da mun gama jin amfaninsu daga bakin wadanda suka yarda da su, bari kuma mu ji ta bakin wadanda suke ganin mace za ta iya rayuwar aure mai kyau ko ba kayan mata.

Likitoci da dama da na zanta da su sun yi matukar gargadi kan yadda mata ke amfani da kayan da'a a zamanin nan 'ba kai ba gindi.' Sun ce kayan da'a na lalata yanayin halittar jiki mai kyau da Allah ya yi wa mata tare da yi musu illa in ba a dace ba.

Kwararru a fannin kiwon lafiya na ganin maimakon mata su yi ta dirkawa kansu hade-haden da ba su san mene ne ba gara su yi ta cin kayan marmari da ganyayyaki masu gina jiki.

'Kayan marmari kawai sun isa su bai wa mace irin ni'imar da take bukata wacce za ta gamsar da mijinta ba tare da shan kayan mata ba,' in ji wata likita.

Wata ungozoma da na taba hira da ita ma ce min ta yi, "ba za ki ga kayan takaici ba sai kin zo karbar haihuwar masu irin wannnan shaye-shayen kayan matan, sai ki ga kazanta da datti na fitowa daga al'aurarsu, duk sun cusa abubuwan da ba su san da me aka hada ba sun zame musu cuta."

Na yi hira da wasu matan da ba su da ra'ayin wannann harka in da suka ce su wasan yara suka dauki batun maganin mata, yana maka aiki ne kawai idan ka yi imani da shi.

A tattaunawar da na yi da wasu mazan, sun nuna suna ganin amfanin su idan matansu suka yi. Wasu ma su suke sayawa matan da kudinsu ko nawa ne kuwa.

Yayin da wasu kuwa ke kyankyamin abubuwan kuma ba sa so matansu su yi amfani da su sam.

Ni dai a nawa ra'ayin, ina tababa ko wannan kayan matan sun kai a dinga bare-baren jiki wajen amfani da su da kuma kashe makudan kudi, ganin cewar aikinsu na dan lokaci ne. Ku meye naku ra'ayin?