Mene ne sirrin birnin kasar Habashar da a ke kira Makkar Afirka?

Harar street scene

A daidai lokacin da birnin Harar wadda hukumar raya al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta san da zamanta ke bikin cika shekara 1,010 da kafuwa, wakilin BBC, Emmanuel Igunza, ya yi nazari kan kayayyakin tarihi na birnin da suka fita daban.

Da faduwar rana a birnin Harar, na ga wani abin mamaki, in ba abin almara ba ne.

Wani matshi ya soke nama da kara. Ya rike karan a bakinsa sannan ya fara ciyar da wasu kuraye da suka fito daga cikin duhu idanunsu na walkiya da suka fito cikin haske.

"Ina yin haka ne domin ina son dabbobi," In ji Biniam Ashenafi, dan shekara 32 daya daga cikin masu aikin sa kai da ke ciyar da kurayen a ko wacce rana.

Bayanan bidiyo,

Mutumin da ke bai wa kuraye nama a baki

"Ba ma ce musu kuraye. Muna ce musu kananan limamai ne. A ko wacce sabuwar shekara a ta Musulunci, muna musu walimar fate a kusurwowi hudu na birnin.

"In suka amshi abin da muka basu, yana nufin gaba za ta yi kyau kenan. Idan suka ki, yana nufin wani abu mara kyau zai faru."

Mutane a birnin Harar sun shafe daruruwan shekaru suna zama da kuraye, daya daga cikin namun dajin da suka fi kisa a duniya.

Harar - tarihi mai tsawo:

  • Karni na Bakwai: Wani bangare na daular Kiristoci Kibdawa ya karbi Musulunci.
  • 1007: An kafa birnin Harar
  • Karni na 16: Ya zama babban birnin masarautar Harari, muhimmiyar cibiyar kasuwanci da ilimin addinin Islama a yankin
  • Wasu na cewa shi ne wuri na hudu da ya fi tsarki a addinin baya ga Makka da Masallacin Kudus da kuma Madina
  • 1887: Ya zamo wani bangare a kasar Habasha
  • 2006: Hukumar Raya Al'aldu da Ilimi da Kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware shi a matsayin wurin tarihi

Ganuwar birinin, wadda aka gina a karni na 13 da na 16, suna da kananan kofofi a jikinsu domin kuraye su samu damar shiga birnin da daddare.

Bai wa kura abinci daya ne daga cikin al'adun da suka sa birnin ya fita daban.

"Wannan daya ne daga cikin dadaddun al'ummomi da suka kafu tun farko-farkon zamani," in ji masanin tarihi a birnin, Abdulswamad Idris.

"An gina wasu daga cikin masallatan da ka ke gani a nan ne a karni na 10."

Daya daga cikin wadanda suka fara karbar Musulunci

Harar birni ne mai sunaye daban-daban daga birnin ma'asumai zuwa birnin tarihi, yayin da wasu suke masa ganin wuri na hudu mafi tsarki a Musulunci bayan Makka da Masallacin Kudus da kuma Madina.

Kazalika an kira shi birnin lumana, wani suna da na gani a kan wani babban allon sanarwa na lantarki a lokacin da nake shiga birnin.

Dubban mutane daga kasar tare da masu yawon bude ido daga wasu kasashe suna hallara a nan domin bikin cikar Harar Jugol - sunan da ake kiran birnin mai ganuwa a hukumance - shekara 1,010 da kafuwa.

Wani mai yi wa masu yawon bude idanu ja gaba, Dagnachew, ya tambayeni: "Ta ina ka ke son ka fara yawonka?"

"Lallai masallacin zan fara zuwa," na fada cikin sauri.

"Amman wane masallacin?" ya mayar min da martani yana dariya. "Akwai daruruwan masallatai."

Daya lakabin Harar din shi ne Makkar Afirka, kuma mutane a nan suna ikirarin cewar mazauna wurin sun karbi addinin Musulunci ne shekara takwas kafin mutanen birnin Madina na a Saudiyya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masalllacin Jimma shi ne masallaci mafi girma a Harar

An ce sahabban Annabi (SAW) sun yi hijira daga Makka a farkon karni na bakwai kuma aka karbe su a masarautar Axum, wurin da a yanzu ya hada da kasar Habasha da Etitriya.

"Mutanen Harar da na Harlaa sun kai shekara 7,000. Amman birnin kansa ya samu kafuwa ne shekara 1,010 da ta gabata," in ji Mista Abdulsamad.

Fiye da shekara 40 a karni na 16, garin ya kasance babban birnin masarautar Harari, kafin ya zama wani bangare na kasar Ethiopia a shekarar 1887.

'Yan uwantaka

Yau shi ne babban birnin jihar 'yan kabilar Harari, jiha mafi karancin al'umma a kasar Ethiopia.

A shekarar 2006, Hukumar Raya Al'adu da Ilimi da kuma Kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tsarin gine-gine na birnin da ya fita daban wanda ya hada al'adun Afirka da na Islama na mazauna wurin.

Da nake tafiya a shahararrun lungunan birnin, na ga abin da yake jan mutane zuwa nan. Sauyi kadan aka samu tun da.

Da na sha kwana sai na ji gomman kekunan dinki suna ta aiki.

"Wannan titin ya yi suna domin kayayyakin da ake dinkawa a wurin," in ji Dagnachew , yana nuna min kayayyaki masu launi mai haske da kuma rigunan da aka baje-kolinsu a a kananan shaguna.

Wani abin jan hankali shi ne gidan kayayyakin tarihi da mawakin Faransa, Arthur Rimbaud wanda ya zauna tare da aiki a matsayin dan kasuwa a Harar ya kafa a karni na 19.

Hotunan da ke gidan tarihin yawancin su hotuna ne marasa launi wadanda tsufansu ya kai farkon shekarun 1900.

Hotunan baki da kuma shugabannin birnin sun cika hotunan da ke gidan tarihin wadanda suka hada da hotunan kasuwanni da majami'u.

Daga cikin bakin akwai matasa 'yan asalin kasar Ethiopia da suka shigo daga kasashen waje.

"Bana jin akwai wani wuri kamarsa a duniya," in ji Sayo Addous, wanda aka haifa a Harar kuma a yanzu haka yake zama a Birtaniya.

"Birnin na da karfin 'yan uwantaka na iyali, wanda nake ji ba a samu sosai a karni na 21 ba."