'Inshorar lafiya ka iya maye gurbin da zumunci ya bari'

  • Mukhtar Adamu Bawa
  • BBC Hausa
National Hospital Abuja

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babban asibitin kasa na Abuja na daga cikin asibitocin da suka fi yawan ma'aikatan da ke zuwa karkashin tsarin inshorar lafiya ta kasa

Mutane da dama na tambayar shin mece ce inshorar lafiya? Sai ma'aikatan gwamnati ne kadai za su iya cin moriyarta? Mene ne amfanin shirin ga masu karamin karfi?

Wani bayani da hukumar inshorar lafiya ta Najeriya ta wallafa a shafinta na intanet ya ce, "An kafa hukumar ce a karkashin dokar inshorar lafiya ta kasa, Cap N42, cikin dokokin Tarayyar Najeriya na 2004, da nufin samar da hanya cikin sauki ta samun kula da lafiya ga dukkanin 'yan Najeriya a cikin farashi mai rahusa ta hanyar tsare-tsare iri daban-daban na biyan kudi kafin zuwa asibiti..."

Shirin inshorar lafiya, a cewar Farfesa Usman Yusuf, kamar wani asusu ko adashi ne, inda mai lafiya zai taimaki maras lafiya, mai karfi ya taimaki maras karfi.

"Kusan duk lungunan Najeriya da ka je, za ka iya samun maras lafiya, amma saboda rashin halin zuwa asibiti sai su zauna a gida su yi ta wahala".

"A da, lokacin da zumunci yake da karfi, 'yan'uwa ne suke kawo gudunmawa idan wani ya shiga halin rashin lafiya, sai dai yanzu zumunci ya yi karanci, 'yan'uwa sun yi nisa da junansu," in ji wani malamin addinin musulunci a Abuja, Sheikh Hussaini Zakariyya.

A wata hira da ya yi da BBC a baya-bayan nan, dakataccen manajan daraktan hukumar inshorar lafiya ta Najeriya, Farfesa Usman Yusuf ya karfafa wannan batu da cewa, "Tun muna yara muke asusu, kuma dukkanmu muna daukar nauyin 'yan'uwanmu da ba su da lafiya."

Ya ce amfanin shirin inshorar lafiya, shi ne taimaka wa jama'a su samu halin zuwa asibiti.

Wane ne ya cancanci shiga?

A cewar Farfesa Usman Yusuf, kamata ya yi hukumar inshorar lafiya ta iya kula da duk al'ummar Najeriya kimanin miliyan 170, ko da yake, bayan shekara 11 da bude ta, mutum miliyan biyu ko uku kadai ne ke cikin shirin.

Bayanan hoto,

Farfesa Usman Yusuf ya ce akwai wani shirin inshorar lafiya na al'umma (musammam mazauna yankunan karkara) wato Community based health insurance

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Hukumar inshorar lafiya wadda aka kafa tun 1999, na da tsarin cire wani kaso na albashin ma'aikatan gwamnati don sanya wa cikin asusunta ta yadda idan su ko iyalansu ba su da lafiya, za a biya musu kudin magani.

Sai dai, bayan shekaru hukumar ta fahimci cewa ma'aikatan gwamnati su kalilan ne, idan an kwatanta da daukacin al'ummar Nijeriya.

Don haka hukumar inshorar lafiya ta kasa ta bullo da shirye-shirye da dama, don mutanen da ba sai lallai ma'aikatan gwamnati ba su amfana.

Farfesa Usman Yusuf ya ce akwai wani shirin inshorar lafiya na al'umma (musammam mazauna yankunan karkara) wato Community based health insurance.

Shirin ya tanadi wani tsarin karo-karo a tsakanin mazauna yankunan karkara, inda mutum zai rika biyan naira 150 duk wata don tarawa a sanya hannun wata gidauniyar da za a rika ajiyewa a banki.

Haka zalika, akwai wani shiri mai suna Voluntary Contbutorship ga mutanen da ba ma'aikatan gwamnati ba.

Ya ce a shekara ana zuba naira 15,000 wato naira 41 a kullum, idan ka biya wa wani zai iya zuwa asibiti kamar yadda za ka je ka ga likita.

Su wane ne ke cin gajiyar shirin?

Akasarin masu cin gajiyar shirin a cewar Farfesa Usman Yusuf, su ne ma'aikatan gwamnatin tarayya, wadanda ake cire wani kaso na albashinsu a matsayin gudunmawa.

Ya ce shugabancinsa yana kokarin fita daga Abuja, don shiga garuruwa da kauyukan da ke fadin kasar.

Haka zalika, wasu malaman makarantun firamare da na lafiya da ke aiki karkashin kananan hukumomi a jihohin Bauchi da Kano da Kwara sun shaida wa BBC cewa ba sa cin gajiyar shirin.

Shirin na kula da kowacce cuta?

Farfesa Usman Yusuf ya ce akwai cutuka masu tsadar magani wadanda ba yadda za a yi wannan shirin, ya iya biya musu (kudin magani).

Cutuka irinsu haihuwa da awon ciki da larurorin kananan yara da hauhawar jini da ciwon suga da sauran cutukan mutane na yau da kullum duk muna biya, in ji shi.

Ya ce yana fafutukar sanar da gwamnati cewa akwai cutuka masu tsadar magani, don ta shigo ta taimaka wa hukumar inshorar lafiya don ganin an agaza wa masu irin wadannan cutuka.

"Kamar masu cutar daji, ina ganin mata da maza masu cutar daji, da masu ciwon koda, amma wannan shirin ba ya iya kula da su. Saboda idan an yi, to duk sai an kwashe kudin da aka sanya a asusun.

Yaya shirin ke aiki?

Bayani a shafin hukumar inshorar lafiya ta kasa ya nuna cewa shirin na da masu ruwa da tsaki kamar haka:

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sai dai ba kowanne tsarin kula da lafiya ne shirin ke samar wa ma'aikata ba

Gwamnati: Ta hanyar Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa ita ce ke da alhakin tsara ka'idoji da tanade-tanade, a lokaci guda kuma tana kare hakkoki da tabbatar da ganin duk masu ruwa da tsaki na sauke nauyin da ke kansu.

Ma'aikata: Wadannan su ne masu ba da gudunmawa a cikin shirin... Gudunmawar (kashi biyar na tsagwaron albashinsu), da suke biya duk wata zai ba su, da su da iyalansu damar samun kula da lafiya mai inganci a duk lokacin da suka kamu da rashin lafiya.

Iyayen gidan ma'aikata: Wadannan cibiyoyi ne na gwamnati da masu zaman kansu da ke da ma'aikaci goma (10) ko fiye, wadanda kuma ake bukatar su biya musu gudunmawar (kashi 10% na tsagwaron albashin da ma'aikaci ke dauka).

Sauran masu ba da gudunmawa: Wadannan sun kunshi bangarorin da ke yin karo-karo na kudi kalilan da za su iya a cikin shirin inshorar lafiya don kula da masu sana'o'in kai-da-kai a birane, da kuma cikin asusun kula da al'ummomin yankunan karkara don samun tsarin kula da lafiya mai inganci a duk lokacin da suka kamu da rashin lafiya.

Dillalan shirin inshorar lafiya (HMO): Wadannan wasu kamfanoni ne da cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu har da daidaiku suka kafa da nufin taimakawa wajen cin moriyar shirin ga masu ba da gudunmawa.

Kwamitin amintattu (BOTs): Mutanen da ke cikin shirin kula da lafiya masu sana'o'in kai-da-kai a birane da al'ummomin yankunan karkara ta hanyar zababbun kwamitocin amintattu, ka iya shiryawa da kula da gudanar da shirin kula da lafiyarsu.

Cibiyoyin kula da lafiya : Wadannan sun kunshi asibitocin gwamnati ko masu zaman kansu da gwamnati ta yi wa lasisi kuma hukumar inshorar lafiya ta yi musu rijista don kula da lafiyar masu ba da gudunmawa da iyalansu a cikin shirin. Asibitocin kuma sun kunshi kanana da matsakaita da manya.

Matsayin shirin a Musulunci

Masu ruwa da tsaki na bayyana damuwa a kan karancin masu cin gajiyar shirin inshorar lafiya a Najeriya duk da dumbin alfanunsa.

Farfesa Usman Yusuf ya ce saboda haka ne ma, shugabancinsa ya dukufa wajen fadakar da jama'a kuma a baya-bayan nan har ya kai ziyara Sakkwato, kuma Sarkin Musulmi da Sarkin Gwandu sun tara masa malaman addinin musulunci.

A cewarsa, malaman sun ba da fatawa cewa asusun inshorar lafiya, bai saba wa musulunci ba.

Haka zalika, BBC ta tuntubi Sheikh Hussaini Zakariyya, malamin addinin musulunci a Abuja wanda ya ce musulunci gaba dayansa, masalaha ce ga musulmi, don haka duk abin da zai janyo wa musulmi alkhairi, da zarar an bi dokoki da ka'idoji, ana iya aikata shi.

Ya ce batun inshorar lafiya ana iya sanya shi cikin babin Atta'a'wun.

A cewarsa, an so musulmi su zo su taimaka wa junansu a lokacin da ake bukatar taimakon da kuma gudunmawa.

"Idan mutum ya shiga wani halin ni-'ya-su ko na-kasa saboda rashin lafiyarsa ko kuma iyalansa, babu wani abin da musulunci ya hana a taimaki juna ko a yi gudunmawa idan aka shiga halin bukata."

"Dole a samu wata madafa ko wani dandali da zai maye gurbin wadannan 'yan'uwan, wajen kawo gudunmawa lokacin da ake bukata.

Ka ga kenan wane ne zai haramta wannan ko ya ce wannan ba daidai ba ne."

Kalubalen shirin a Najeriya

Daya daga cikin manyan kalubalan shirin inshorar lafiya shi ne karancin masu cin gajiyarsa.

Farfesa Usman ya ce manufar shugabancinsa ita ce fita daga Abuja, su kusanci jama'a a garuruwa da kauyuka kuma ya kawar da cin hanci da rashawa a hukumar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu ma'aikatan gwamnatin sun koka kan yadda ba a ba su kulawar da ta dace kamar ta sauran mutanen da ke biyan kudi kai tsaye daga aljihunsu

Ya koka kan yadda wasu jami'ai ke almubazzaranci da dukiyar jama'a. "Wadannan dillalai ba sa biyan asibitoci, asibitoci ba sa kula da jama'armu, likitoci ba sa kula da jama'armu, mu hukumar inshora da ya kamata mu tabbatar sun yi aikinsu ba ma yi."

Ya ce ba gaskiya ba ne zargin cewar hukumar inshorar lafiya ba ta biyan dillalan shirin kudadensu a kan lokaci. Tun lokacin da aka fara shirin inshorar lafiya a Najeriya shekara 11 da ta wuce, hukumar ba ta fashin biyan wadannan dillalai, a cewarsa.

Ya ce hukumarsa tana biyan kudin dillalan wata uku kafin mutum ya je asibiti. BBC ta yi kokarin jin ta-bakin daya daga cikin irin wadannan dillalai a Abuja, sai dai kamfanin ya ki amincewa ya yi bayani.

Farfesa Usman Yusuf kuma, ya koka game da rashin wayar da kan al'umma kan dumbin alfanun shirin.

"Abin da hukumar inshorar lafiya ke yi don taimakon kai-da-kai ne. Sannan kuma mu wannan hukuma muna kokarin ganin mun yi wa jama'a adalci.

Jama'a su tara kudinsu, kudin amana, amma a zo ana almubazzaranci da dukiyarsu? Idan ba ka tabbatar za ka iya rike amanar jama'a ba, to ina amfani?

'Zuma da madaci'

Wasu ma'aikata da suka yi rijista da shirin a Abuja, Mallam Abdulkadir Abubakar da Aisha Ibrahim sun ce inshorar lafiya ta kawo musu sauki wajen sayen magunguna da biyan kudin aiki, a duk lokacin da suka je asibiti musammam a birni mai tsadar rayuwa kamar babban birnin Nijeriya.

Ma'aikatan suka ce ko da yake, shirin inshorar ya ba su zabin asibitin da suka ga dama, ko da na kudi ne, amma ba a nan gizo yake saka ba.

A cewarsu, ana nuna musu fifiko da masu cin gajiyar shirin da suka fito daga kamfanoni da kuma wadanda suke biyan gudunmawa da hannunsu ta hanyar ba su kulawa ta musammam kuma a kan lokaci. Matsalar da suka ce ba su san daga inda ta faro ba, kuma ko sun yi korafi ba sa ganin sauyi.