Kun san mutumin da ke bai wa kuraye nama a baki?

Kun san mutumin da ke bai wa kuraye nama a baki?

Mutanen da ke zaune a garin Harar na kasar Habasha mai tsohon tarihi ba sa jin tsoron kurayen da ke gararamba a titunan garin.

Har sunaye suke ba su, kuma akwai mutane na musamman da ke abota da kurayen wadanda ke ciyar da su danyen nama, inda suke sa shi a bakinsu sai tura bakin kurayen.