India: Ana bai wa fasinjojin jirgin kasa gurbataccen abinci

Food served on an Indian train
Bayanan hoto,

Fasinjoji na yawan korafi kan rashin tsaftar abincin

Wani rahoto da hukumomin Indiya suka fitar, ya ce abincin da ake ba fasinjojin jiragen kasa da kuma na tashohin jiragen kasa ba mai inganci ba ne.

Rahoton ya ce, a binciken da hukumomin suka gudanar, cikin jiragen kasa 80 da kuma tashohin jiragen kasa 74 sun gano cewa, ana bayar da gurbattacen abinci, yayin da wadanda ake kunshewa cikin leda da kuma ruwan roba suka lalace.

Hukumar jiragen kasa ta Indiya ta ce ta dauki matakin 'ba sani ba sabo' domin tabbatar da ingancin abinci, kuma ta soke aikin kwangilar da ta bai wa wasu kamfononi wadanda ake zarginsu da bayar da gurbataccen abinci.

Sun kara da cewa ana ajiye abincin a budadden waje inda beraye da kudaje ke hawa kai.

Indiya na daya daga cikin kasashen da ke da hada-hadar sufurin layin dogo mafi girma a duniya, inda fasinjoji kusan miliyan 23 ke zirga-zirga a kullum.

Harkar sufurin jirgin kasa ita ce kashin bayan ci gaban sufurin kasar, wanda yawanci an gina layukan dogon ne tun lokacin da Turawa ke musu mulkin mallaka.

Amma fasinjoji na yawan sukar yadda ake bayar da abinci a jiragen, kuma hukumar layin dogo ta sanar da sabon tsarin bayar da abinci a jiragen a watan Fabrairu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar jiragen kasa ta ce ta kaddamar da sabon tsari da zai kawo sauyi

Rahoton ya gano cewa:

  • Ana amfani da ruwa marar tsafa wajen yin lemukan sha
  • Ana yawan barin bola ta taru kuma ba a kawashe ta da wuri
  • Ana barin kayan abinci a bude ta yadda kudaje da kwari da kura ke hawa kai
  • Ana samun kyankyasai da beraye a cikin jiragen kasa

Rahoton ya zargi hukumar jiragen kasa da cewa sun kasa samar da kicin da wajen raba abinci mai kyau.

Sai dai a ranar Juma'a hukumar kula da jiragen kasan ta ce a sabon tsarin nata da ta kaddamar a watan Fabrairu, za ta tabbatar da bai wa fasinjoji ingantaccen abinci.

Ta yi alkawarin yin sabbin kicin don maye gurbin tsoffin.