Yadda makadi ya kada jita ana masa tiyata a kwakwalwa

Mr Prasad undergoing surgery

Asalin hoton, PTI

Bayanan hoto,

Mista Prasad ya ce ya ji garau yayin da ake masa tiyata

Wani mawakin kasar Indiya ya rika kada jita a lokacin da ake yi masa tiyata, domin taimaka wa likitocin lura da motsin 'yan yatsunsa

An bukaci Abhishek Prasad ya rika kada jita yayin da likitocin ke "gasa" kwakwalwarsa bayan yi masa tiyata wani ciwo da yake fama da shi.

Yanayin yana jawo ciwo duk lokacin da mai fama da cutar yake kwance.

Mista Prasad ya shaida wa BBC cewa yana iya kada jitar a hankali bayan tiyatan.

"A yayin da aka yi gashi a karo na shida, 'yan yatsuna sun bude. Ina iya amfani da jitar kanta," Mista prasad ya ce bayan da likitocin suka kwance zaren dinkin da ke kansa ranar Alhamis, mako daya bayan an yi masa tiyatar a kudancin birnin Bangalore da ke kasar Indiya.

Cutar ta hana Mista Prasad motsa wasu daga cikin 'yantsunsa a duk lokacin da yake kada jita.

"Na zaki taurin da yatsana yake saboda yawan kada jitar da nake yi. Sai na dan dakata, na huta amma kuma sai abin ya ki yin sauki. Daga nan ne sai wasu likitoci suka ce min gajiya ce kuma sai aka ba ni maganin kashe zafin ciwo da wasu magunguna," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa 'yatsansa na ciwo ne kawai idan yana kada jita.

Kimanin wata tara da suka wuce ne likitocin kwakwalwa suka gano cewa Prasad yana fama da ciwon Dystonia.

"Sai aka ba ni shawara kan na je a yi min aiki a kwakwalwa, amma sai na tsorata. Likitana Sharan Srinivasan shi ne ya ba ni kwarin gwiwa kan na yarda a yi min aikin," in ji shi.

'Kamar na'urar janareta'

Mawakin ya ce ya rika tuna matakan da ake bi wajen kada jita.

Ya ce likitoci sun sanya wasu na'urori guda hudu a kansa, suka dauki hoton kansa kafin suka buge kwakwalwarsa.

"Hoton kan da aka dauka yana taimakawa wajen gane hanyar da ta dace a tafiyar da aikin," in ji Prasad.

Ya ci gaba da cewa "na ji kamar an kunna na'urar janareta yayin da ake aikin", amma kuma "babu wani zafi da na ji".

Asalin hoton, Imran Qureshi

Bayanan hoto,

Makadin ya ce ya kada jitar ne jim kadan bayan kammala aikin tiyatar

Dokta Srinivasan ya yi karin bayani inda ya ce: "wanda ake wa aikin ba zai ji zafi ba koda kankani saboda yadda ake kashe zafin ciwon".

Ya kara da cewa mun haka wani dan karamin rami a kwakwalwarsa "inda muka sanya wasu kananan na'urori a ciki".

"Idonsa biyu yayin da ake aikin kuma an gane cewa an yi nasara ne bayan da ya fara amfani da 'yantsunsa," in ji likitan.

Mista Prasad ya ce: "ina jin kasala a hannuna na hagu da kuma kafata ta hagu yanzu."

"Amma zan warware a cikin wata guda kuma sai na fara kada jita kamar yadda na saba," in ji Prasad.

Dokta Srinivasan ya ce aikin tiyatar da aka yi a kasar Indiya ba karamin nasara ba ne.

A karshe ya ce: "Masu fama da irin wannan cutar suna shiga halin kadaici. Kuma muna fatan kaiwa gare su."