Nigeria: Kotu ta daure Basaraken da ya kitsa sace kansa gidan yari

Lagos
Bayanan hoto,

Basarake Yusuf Ogundare (daga dama) tare da kaninsa Mohammed Adams

Wata kotun majistiri a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, ta bayar da umarnin ci gaba tsare basaraken da ake tuhuma da kitsa sace kansa don neman kudin fansa a gidan yarin Kiri-kiri da ke jihar.

A makon jiya ne gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya dakatar da Basarake Yusuf Ogundare, wanda shi ne basaraken Shangisha a Magodo da ke cikin jihar Legas saboda kitsa shirin sace kansa da kaninsa don neman kudin fansa.

Basaraken ya bayyana a gaban kotun tare da uwargidansa Abolande da kuma kaninsa Mohammed Babatunde.

Kotun wadda ta yi zama a ranar Alhamis, ta yi umarni da ci gaba da tsare su duka har sai sun iya cimma sharuddan da aka gindaya musu na beli.

Daga nan ne sai kotun ta dage zamanta zuwa ranar 23 ga watan Agusta mai zuwa.

A ranar 5 ga watan Yuli ne basaraken ya bace a cikin karamar hukumar Ikosi-Isheri ta jihar Legas.

A sanadiyyar wannan ne gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya dakatar da basaraken daga aiki.

A wata sanarwar da kwamishinan kananan hukumomi da al'ummomi ya sanya wa hannu, ta ce gwamnan ya dakatar da basaraken daga aikinsa.

"Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya bayar da umarnin dakatar da Chief Yusuf Ogundare, basaraken Shangisha nan take".

"A sanar da shi cewa gwamnatin jihar Legas tana gargadinsa da ya daina nuna kansa a matsayin basaraken Shangisha daga yanzu", in ji sanarwar.

Kafin wannan sanarwar, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Fatai Owoseni, ya nuna wa manema labarai basaraken tare da Mohammed Adams, wanda 'yan sanda ke tuhuma da taimaka wa basarake Ogundare wajen aikata wannan laifin.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"A ranar 11 ga watan Yuli da misalin karfe 10 na dare, wasu jami'an 'yan sanda masu sintiri sun ga wata mota ta sauke wani mutum kusa da kantin Shoprite da ke kusa da titin Sakatariya, in ji kwamishinan 'yan sandan.

"Irin gudun da motar ta yi bayan sauke mutumin ya ba jami'anmu dalilin karasawa wurin, inda suka taras da basaraken da a ka ce an sace ne".

Bayan an kammala bincike ne jami'an tsaro suka tabbatar da cewa babu gaskiya a cikin batun satar.

"A ranar da muka sami rahoton cewa an sace basaraken a Legas, bincike ya tabbatar cewa ya na cikin birnin Ibadan kusa da unguwar Ashi, daga nan kuma ya wuce zuwa Ilorin, da Iwo, watau ya fita shakatawarsa ne kawai", in ji sanarwar ta 'yan sanda.

Binciken na jami'an tsaro ya kuma gano cewa bayanan da suka samu daga matar basaraken da kaninsa sun sha bam-bam da juna.

A halin yanzu matar basaraken da kanin nasa suna hannun 'yan sanda, har sai an kammala binciken irin rawar da suka taka.

Gwamnatin jihar Legas tayi tir da halayyar wannan basaraken, inda ta ce abin da ya yi abu ne marar kyau, musamman ma a wannan lokaci da jihar ke fama da karuwar ayyukan manyan laifuka kamar fashi da makami da garkuwa da mutane.

A kwanan baya ne aka sace wasu 'yan makaranta shida daga wata makaranta dake jihar Legas, inda masu garkuwa da 'yan makarantar suke neman a biya su kudin fansa kafin su sake su.